News
Gwamnatin Kano za ta Inganta Bangaren Sashin Samar Da Magungunan Jihar
DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
An jaddada kudurin Gwamnatin Alhaji Abba Kabir Yusuf na inganta bangaren samar da magunguna da da ke Hukumar Samar da Magunguna (DMCSA) na Jihar Kano.
Kwamishinan Lafiya na Jihar, Dakta Abubakar Labaran Yusuf ne ya bayyana hakan a ranar Talatar da ta gabata a lokacin da yake kaddamar da kwamitin da duba hanyoyin inganta sashin da ke samar da magunguna da kuma kwamitin da zai yi nazarin hade shirin samar da magunguna masu rahusa na KSCHMA da kuma DRF na asibiti.
Gwamnatin Jihar Kwara Ta Bayyana Shirinta Na Kawar Da Bahaya A Bainar Jama’a A Fadin Jihar
An gudanar da taron ne a harabar hukumar DMCSA da ke cikin garin Kano.
Hakan na kunshe ne ta cikin wata Sanarwa da Jami’in yada labarai na Ma’aikatar Lafiya Ibrahim Abdullahi ya turawa da Jaridar Inda Ranka.
Sanarwar ta kara da cewa Kwamishinan ya ce, sashin DMU na da matukar muhimmanci saboda yana samar da magunguna a cikin gida, haka ne ya sa gwamnati mai ci za ta tabbatar da cewa sashin ya ci gaba da samar da magunguna masu inganci.
Dakta Labaran ya ce manufar ita ce kare al’ummar jihar nan daga shan magungunan da ba su da inganci da kuma jabun magunguna da ke yaduwa, inda ya tabbatar da cewa ta hanyar inganta sashin DMU, jihar za ta samu karin hanyoyin samar da magunguna, kuma sashin zai samu karfin gwiwar samar da muhimman magunguna da ake bukata a jihar.
Kwamishinan ya tabbatar da cewa ta wannan hanya asibitoci mallakin gwamnati da asibitoci masu zaman kansu da ke sha’awa za su rinka sayen magunguna daga DMCSA saboda inganci da araha.
Dangane da hadr KSCHMA DRF da DRF na asibiti, Dakta Labaran ya ce haɗewar na da muhimmanci saboda zai ba da kyakkyawar fahimta game da abubuwan da ke faruwa a DRF na KSCHMA.
Ya jaddada cewa hadawar zai ba da damar habaka samar da magunguna masu inganci da araha ga abokan huldar KSCHMA.
Dakta Labaran ya ci gaba da cewa an dauki matakin ne don sauya yanayin rashin isassun magunguna masu inganci ta hanyar tabbatar da cewa ana samar da magungunan da suka dace ga abokan huldar KSCHMA a cibiyoyin lafiya a ko da yaushe.
Daga nan sai ya bukaci mambobin kwamitocin da su ba da muhimmancin gaske ga aikin da aka ba su, domin zai yi tasiri ga rayuwar al’ummar jihar.
Tun da farko, Darakta Janar na DMCSA, Pharm. Gali Sule ya jaddada cewa, samar da magunguna na daga cikin ayyukan hukumarsa, yana mai cewa sashin DMU ya shafe sama da shekaru 30 yana samar da magunguna.
Ya yi nuni da cewa ana bukatar a sake duba ayyukan sashin na DMU ne domin a bi dukkan ka’idojin da Hukumar Koli ta Samar da Magunguna da NAFDAC suka tanada.
Shugaban hukumar ya ce kwamitin ya kunshi masu ruwa da tsaki daga sassa daban-daban, kuma gwamnati na da yakinin cewa mambobinsa za su fito da wata shawara da rahotanni da za su taimaka wajen inganta sashin zuwa matsayin ayyukan da dukkanin hukumomin da suka dace suka shimfida.
Shugabannin kwamitocin, Farfesa Bashir A. Chedi da Pharm. Abdullahi Abubakar Danzabuwa, a madadin sauran mambobin, sun ba da tabbacin yin aiki tukuru domin tabbatar da amincewar da aka yi musu, tare da mika rahoton farko na aikin a lokacin da aka ba su.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
