News
Hukumar Filayen Jiragen Saman Nijeriya FAAN ta haramta amfani da jakar Ghana Must Go
DAGAKABIRUBASIRUFULATAN
Hukumar kula da filayen jiragen sama ta Najeriya (FAAN) ta haramta amfani da buhunan ‘Ghana Must Go’ da fasinjoji ke yi a dukkan filayen jiragen saman kasar.
A wata sanarwa da FAAN ta fitar mai taken, ‘Re: Prohibition of Use Of Ghana Must Go’, mai dauke da sa hannun Manaja, Ma’aikatar Jiragen Sama, Henok Gizachew, ta ce haramcin ya shafi fasinjojin da ke bi ta filayen jiragen sama na kasa da kasa.
Kada Wanda Ya Karkatar Da Kudaden Da Aka Ware Wa Fannin Tsaro- -Shehu Sani
Gizachew ya bayyana cewa hukumar ta hana amfani da buhun ne saboda ya jawo hasarar da kamfanonin jiragen sama suka yi da kuma lalata na’urar daukar bel na filayen jiragen sama.
Ya lura cewa fasinjojin da ke son yin amfani da ‘Ghana Must Go’ don yin balaguro suna janyo lalacewar wasu naurori masu tantance kaya a filayen jiragen saman Nijeriya.
Daily Post ta ruwaito cewa An alakanta amfani da jakunkunan ‘Ghana Must Go’ da lalacewar na’urorin jigilar dakunan jiragen sama na kasar da dama da kuma wanda ya jefa makudan kudade a wuyan hukumar ta filin jirgin.
A wani labarin kuma Kada Wanda Ya Karkatar Da Kudaden Da Aka Ware Wa Fannin Tsaro- -Shehu Sani
Sojojin Isra’ila a yanzu sun ce sun koma yaƙi da Hamas a Gaza.
Jim kadan gabanin cikar yarjejeniyar tsagaita bude wuta na kwanaki bakwai, Isra’ila ta ce ta harba makamin roka daga Gaza yayin da kafafen yada labarai da ke da alaƙa da kungiyar Hamas suka bayar da rahoton tashin bama-bamai da harbe-harbe a arewacin Gaza.
Tun da farko dai an dakatar da tsagaita wuta har na tsawon kwanaki hudu kuma aka tsawaita sau biyu.
Ya zuwa ranar alhamis, an saki fursunoni 110 da aka yi garkuwa da su a Gaza tun lokacin da aka fara tsagaita wuta a ranar 24 ga watan Nuwamba, yayin da Isra’ila ta saki fursunonin Falasɗinawa 240.
Hare-haren Hamas kan Isra’ila a ranar 7 ga Oktoba ya kashe mutum 1,200.
Tun daga wannan lokacin, ma’aikatar lafiya ta Hamas a Gaza ta ce sama da mutum 14,800 ne aka kashe a yakin ramuwar gayya na Isra’ila, ciki har da yara kusan 6,000.
