Connect with us

News

Dan Majalisa Mai Wakiltar karamar hukumar fagge ya gabatar da ko Kensa Bisa Kisan Salisu Player a zauren majalisa

Published

on

Barr. Muhammad Bello Shehu

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN

 

Advertisement

Dan Majalisa Mai Wakiltar karamar hukumar fagge Rt. Hon Barr Muhammad Bello Shehu Ya Gabatar Da Korafi Bisa Kisan salisu player Da Wani jami in Dan sanda Yayi a Unguwar kurna a ranar Talata

Ya Gabatar Da Wannan Korafine Domin Neman Majalisa tayi Bincike Ta Kuma tabbatar Da anyi adalci Kuma An Hukunta Wanda yai Wannan Danyen aiki.

Advertisement

Kasafin kuɗin na 2024 ya tsallake karatu na biyu a majalisun ƙasar nan

Wakilin jaridar Inda Ranka Muhammad Muhammad Zahraddin ya ruwaito cewa Dandazon matasa sun gudanar da wata zanga-zanga a unguwar Kurna da ke tsakiyar birnin Kano, inda suka toshe babban titin zuwa Katsina tun da safiyar Ranar Laraba domin nuna fushinsu a kan harbin wasu matasa.

Sai dai Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta ce tuni an kama dan sandan da ake zargi da yin harbin na ranar Talata, wanda ya kai ga matasan gudanar da zanga-zanga a wayewar gari.

Advertisement

A ciki wata sanarwa da ta fitar, rundunar ta ce dan sandan mai mulkamin sufeto ya yi harbi kan kungiyoyin matasan da ke rikici da juna ne inda ya raunata biyu, daya kuma ya riga mu gidan gaskiya.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, Mohammed Usaini Gumel, ya ba da umarnin gudanar da bincike kan lamarin.

Advertisement

A cewar sanarwar tuni aka kama sufeton, kuma a halin yanzu yana tsare a hannun ‘yan sanda.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending