News
Kasafin kuɗin na 2024 ya tsallake karatu na biyu a majalisun ƙasar nan
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Majalisar Dattawan Najeriya da ta Wakilai sun yi wa kasafin kuɗin ƙasar na 2024 karatu na biyu ranar Juma’a kwana biyu bayan Shugaba Bola Tinubu ya gabatar musu da shi.
A ranar Laraba ne Tinubu ya je majalisar tare da gabatar da naira tiriliyan 27.5 a matsayin kasafin abin da gwamnatinsa za ta kashe a 2024, kuma ya nemi ‘yan majalisar su gaggauta amincewa da shi.
Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta cafke sama da mutane 53 da ake zargi da aikata laifuka
Sai dai shugaban bai bayyana adadin abin da kowace ma’aikata da hukumomin gwamnati za su samu ba a lokacin da ya yi gabatarwar, abin da ya jawo cecekuce da muhawara a ƙasar.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito ‘yan majalisar na kokawa yayin muhawarar da suka yi ranar Juma’a game da ƙarancin bayanai kan kasafin, wanda suka ce ya sa sun mayar da hankali ne kawai kan abubuwan da Tinubu ya faɗa a jawabinsa.
Kundin da gwamnatin ta fitar daga baya ya nuna cewa sashen tsaro ne ya fi samun kaso mafi tsoka na tiriliyan 3.25 – kashi 12 cikin 100 na kasafin ke nan.
Sai kuma ɓangaren ilimi da yake biye masa da naira tiriliyan 2.2, ɓangaren lafiya na da tiriliyan 1.4.
Jam’iyyun adawa sun soki kasafin da cewa “na yaudara ne”, yayin da Shugaba Tinubu ya yi masa laƙabi da “kasafin sabunta fata”.
A wani labarin kuma Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta cafke sama da mutane 53 da ake zargi da aikata laifuka
Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.
Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.
A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.
Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.
