Connect with us

News

Gwamnan Kano Ya Aikawa Majalisar Jihar Karin Kasafin Kudi Na Shekarar 2024

Published

on

Shugaban Kasa Bola Ahmad Tunibu

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN 

Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya gabatar da karin kasafin kudi naira biliyan 99.2 na shekarar 2024 ga majalisar dokokin jihar domin amincewa.

Advertisement

An gabatar da bukatar ne a cikin wata wasika da aka karanta a yayin zaman majalisar wanda kakakin majalisar Ismail Falgore ya jagoranta.

Ruwan Sama Ya Lalata Gidaje, Makarantu Da   Wurare Kasuwancin A Zariya

Gwamnan ya nemi amincewar majalisar ne a karkashin sashe na 122 (A da B) na Kundin Tsarin Mulki na 1999 don gudanar da ayyuka da nufin inganta rayuwar al’ummar jihar.

Advertisement

Kwamishinan tsare-tsare da kasafin kudi Musa Shanono ya bayyana cewa kasafin kudin shekarar 2024 na farko ya kai Naira biliyan 437.3, idan aka kara da wannan karin kasafin ya kai jimillar Naira biliyan 536.5.

Shanono ya jaddada cewa karin kasafin kudin zai kunshi sabon tsarin biyan mafi karancin albashi, samar da ababen more rayuwa, bunkasa rayuwar jama’a da dai sauran muhimman abubuwa.

Advertisement

Ya kuma jaddada aniyar gwamnati na mai da hankali kan wadannan fannoni.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending