News
Ma’aikatar Kananan Hukumomi Ta Kano Ta Gabatar Da Kasafin Kudin 2024 Na Sama Da Biliyan 360
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Majalisar dokokin jihar Kano ta karbi wasika, kan kudirin kasafin kudin kananan hukumomi 44 na shekarar 2024 na sama da naira biliyan 360.
Da yake karantar takardar, shugaban Majalisar Alhaji Jibril Ismail Falgore ya ce ma’aikatar ta ware kaso 49 cikin 100 a matsayin kudaden gudanar da ayyuka, sai kaso 31 cikin 100 na Albashin ma’aikata da sauran hakkokkinsu sai kuma kaso 20 cikin 100 a matsayin kudaden gudanarwa na yau da kullum na ma’aikatar.
Gwamnatin tarraya ta cire harajin VAT na gas din girki ake shigo da shi daga kasashen waje.
Ya jaddada cewa, kananan hukumomi za su bayyana a gaban majalisar a ranar Laraba mai zuwa don kare kasafin kudin.
Golabal Tracker ta ruwaito cewa Majalisar dokokin jihar Kano ta karɓi rahoto game da ƙarin lissafin kasafin kuɗi na 2023 mai lamba 2.
Da yake gabatar da rahoton, shugaban kwamitin riko na majalisar wakilai kan kasafin kudi, Alhaji Aminu Sa’adu Ungoggo ya yi nuni da cewa, kwamitin mambobi 11 sun ba da shawarar amincewa da karin kasafin kudi na naira biliyan 24, domin baiwa gwamnatin jihar damar biyan kudaden fansho na masu ritaya da kuma kammala aikin samar da wutar lantarki a jihar da dai sauransu.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
