Connect with us

News

KHETFUND Ta Taimaka wa Makarantar Fasahar Kiwon Lafiya Da Sama Da N17m

Published

on

Advertisements
ads

DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA

A ci gaba da kokarin aiwatar da daya daga cikin manufofinta, wato tallafa wa cibiyoyin ilmin lafiya, Asusun Tallafa wa Lafiya na Jihar Kano (KHETFUND) ya bai wa Makarantar Fasahar Kiwon Lafiya ta jihar Kano tallafin kudi da ya kai N17,720,000 a kokarin inganta wasu daga cikin kwasa-kwasan makarantar.

An kafa KHETFUND ne musamman don ya rinka samar da karin kudade ga bangaren lafiya da nufin inganta ayyukan kiwon lafiya a cibiyoyin ilimi na lafiya da asibitoci don ci gaban rayuwar al’ummar jihar baki daya.

Hukumar JAMB Ta Musanta Karin Kudin Rijistar UTME Ta 2024

Hakan na kunshe ne ta cikin wata Sanarwa da Jami’in in Yada Labarai na Ma’aikatar Lafiya, Ibrahim Abdullahi, ya turawa da Jaridar Inda Ranka.

Sanarwar ta kara da cewa domin tabbatar da cewa komai ya tafi kamar yadda aka tsara na samun nasarar shirin tantance kwasa-kwasan da suka shafi dakunan gwaje-gwaje, babbar difloma, da difloma ta kasa da kuma bangaren ilimin samar da magunguna, Sakatariyar Zartarwa ta hukumar, Dakta Fatima Usman Zahradeen, ta jagoranci tawagar sa-ido ta KHETFUND domin ganin yadda aka yi amfani da suka bai wa makarantar don samun nasarar tantancewar.

Da take jawabi jim kadan bayan kammala ziyarar, Dakta Fatima ta yaba da gagarumin ci gaban da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya samu na farfado da tsarin kiwon lafiya a jihar, inda ta jaddada cewa mai girma gwamna ya bai wa bangaren kulawar gaske ta yadda cikin kankanin lokaci aka samu gagarumar nasara.

Advertisement

Ta tabbatar da cewa, jajircewar Gwamnan al’umma ne ke ba su kwarin gwiwa (su shugabannin hukumomin lafiya) da su ma su jajirce tare da yin iyakacin kokarinsu wajen bin sawun mai girma Gwamna wajen cika alkawuran da ya daukarwa al’ummar Kano a kan harkar lafiya.

Sakatariyar Zartarwar ta ja hankalin shugabannin makarantar da su tabbatar da cewa an yi tantancewar ba tare da samun wata matsala ba, ta ce hakan shi ne matakin da zai ka ga samar da dalibai masu ilimin da ake bukata na tafiyar da asibitoci idan an dauke su aiki, kamar Gwamna Abba Kabir Yusuf da al’ummar jihar Kano suke fata.

Cikin farin ciki ta bayyana cewa sun bayar da kudaden da ake bukata domin aikin tantance kwasa-kwasan, tana mai jan hankalina da su tabbatar da gaskiya da rikon amana wajen yin amfani da kudaden, domin abubuwan nan biyu suna daga cikin muhimman ka’idojin KHETFUND, tare da fata da kuma addu’ar cewa kwasa-kwasan za su samu nasarar tantancewar.

 

Dakta Fatima ta bayyana cewa samun kudade daga KHETFUND ga wadanda za su amfana daga cibiyoyin ilimin lafiya da asibitoci don aiwatar da ayyuka da shirye-shirye masu ma’ana ba abu ne mai wahala ba, tana mai nuni da cewa an yi bayanin hanyoyin filla-filla a cikin kundin jagorar masu cin gajiyar hukumar da aka gabatar kwanan nan.

 

Advertisement

Daga nan sai ta yaba wa Kwamishinan Lafiya Dakta Abubakar Labaran Yusuf bisa irin nasihohinsa na uba da kuma jagorancin da yake ba su wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyansu, inda ta bayyana shi a matsayin mutum mai hangen nesa, mai kwazo da juriya, wanda ya jajirce wajen ganin an samu ci gaba tare da ganin komai yana tafiya yadda ya kamata a bangaren kiwon lafiya kamar yadda Gwamna Abba Kabir Yusuf ke bukata.

 

Da yake jawabi yayin karbar tawagar, Mataimakin Shugaban Makarantar, ya yaba wa KHETFUND bisa dauki da ta kawo musu, inda ya tabbatar da cewa za a yi amfani da asusun cikin adalci bisa manufar da aka tanada.

 

Ya bayyana cewa Majalisar Koli MSL ta Kimiyyar Gwaje-Gwaje a ranar 15 ga Satumba 2023, ta zo ta tantance kwas din ilimin gwaje-gwaje, sannan ta kammala shirye-shiryenta na samun nasarar gudanar da aikin tantance sauran kwasa-kwasan da suka hada da ND, HND da ilimin hada magunguna tare da fatan aikin zai yi nasara.

 

Advertisement

Ya yaba wa Alhaji Abba Kabir Yusuf bisa yadda ya bai wa bangaren lafiya da ayyukan da suka shafi al’umma da yake aiwatarwa a fadin jihar nan.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending