News
Hukumar JAMB Ta Musanta Karin Kudin Rijistar UTME Ta 2024
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Hukumar shirya jarabawar shiga Jami’ai da sauran makarantun gaba da sakandire ta kasa JAMB ta musanta jita-jitar da ake yadawa cewa ta kara kudin rajistar shekarar 2024.
Mai baiwa hukumar shawara kan harkokin yada labarai, Dr Fabian Benjamin, shine ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a Abuja ranar Laraba.
Rundunar Yan Sanda Sun Bankado Wani Shirin Kona Gidan Gwamnatin Jihar Kano
A cewar Benjamin, bayanan sun sha bamban da gaskiya saboda kudin da ake kashewa wajen Rijistar UTME na hukumar har yanzu dubu 3 da 500 ne.
Benjamin ya kara da cewa sabanin jita-jitar daya daga cikin matakan da Hukumar ta yi la’akari da su shi ne rage farashi a duk wani abu da ya shafi jarabawar ba ya ga kudin rijista.
A wani labarin kuma Rundunar Yan Sanda Sun Bankado Wani Shirin Kona Gidan Gwamnatin Jihar Kano
Rahotanni na cewa shugaban babbar jam’iyyar hamayya ta Najeriya, PDP, Ambasada Iliya Damagum, na fuskantar gagarumin matsin-lamba daga wasu manyan jam’iyyar don hukunta tsohon gwamnan jihar Ribas, kuma ministan babban birnin tarayya Abuja Nyesom Wike, kan zargin yi wa jam’iyyar zagon ƙasa.
Shi dai Wike wanda har yanzu bai sanar da sauya sheƙa daga jam’iyyar ba ya nuna goyon bayansa ne ga Shugaba Tinubu na APC a fili a zaɓen shugaban ƙasar da ya gabata,har ma ya karɓi muƙamin minista a gwamnatinsa, kana daga bisani ya ci gaba da yin abubuwan da wasu ke kallo a matsayin cin dunduniyar jam’iyyar.
A baya-bayan nan ne wasu ‘yan majalisar dokoki 27 na jihar ta Ribas makusantansa, suka fice daga PDP zuwa APC, wani abu da wasu ke kallo a matsayin sharar fage ga shi ma Wiken.
Bayanan da BBC ta samu daga wasu gaggan jam’iyyar ta PDP har da ‘yan kwamitin gudanarwarta, sun nuna rashin jin dadinsu, a kan jinkirin da ake samu, wajen ɗaukar mataki a kan Nyesom Wike.
-
News7 days agoShekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano
-
News3 days agoKotu Ta Daure Wani Limamin Masallacin Juma’a Wata 1 Kan Tura Bidiyon Tsaraici Ga Matar Aure A Kano
-
News5 days agoƘalubalen Da Masu Ƙananan Sana’o’i Ke Fuskanta Saboda Ƙarancin Wutar Lantarki A Kano
