News
Rundunar Yan Sanda Sun Bankado Wani Shirin Kona Gidan Gwamnatin Jihar Kano

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Rundunar ‘yan sanda, ta ce ta gano wani shiri na kona gidan gwamnatin Kano da wasu bata gari ke kitsawa a kan shari’ar da ake ci gaba da yi a kotun koli kan zaben gwamna tsakanin jam’iyyar NNPP da APC.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, Muhammad Usaini Gumel ne ya bayyana hakan a ranar Laraba a wani taro da shugabannin kafafen yada labarai, gabanin zaman kotun koli na daukaka kara kan shari’ar kujerar gwamnan Kano da aka shirya gudanarwa yau Alhamis 21 ga watan Disamba 2023 a Abuja.
An Samu Rahotannin Hatsari Kimanin 231, Yayin Da Mutane 205 Suka Mutu A Jihar Kano
Gumel ya bukaci kwararrun kafafen yada labarai da su sanar da jama’a yadda ya kamata a kan abubuwan da ke faruwa bisa tsari da gaskiyar labari.
A cewarsa bai kamata a samu tashin hankali a Kano ba domin maganar tana kotun koli da ke Abuja ba a jihar ba kamar yanda Arewa Radio ta rawaito
A wani labarin kuma An Samu Rahotannin Hatsari Kimanin 231, Yayin Da Mutane 205 Suka Mutu A Jihar Kano
Ma’aikatan jami’o’i SSANU sun nemi shugaban ƙasa, Bola Tinubu da ya dube su ya biya su albashin su na watanni huɗu da gwamnatin da ta shuɗe ta rike bata biya su ba.
Ma’aikatan sun yi roƙon ne a wani taron majalisar zartarwa ta ƙasa, inda suka ce biyan kuɗaɗen zai taimaka wa mambobinsu gudanar da bikin Kirsimeti yadda ya kamata.
Shugaban kungiyar Kwamared Mohammed Ibrahim a cikin wata sanarwar da ya fitar a ƙarshen taron wanda ya aikawa jaridar Daily Trust a daren ranar Talata, inda ya bukaci Shugaba Tinubu ya cika alƙawarin da ya dauka na biyan mafi ƙaranchin albashi na N35,000.
In ba a Manta ba kwanakin baya Wikkitimes ta ruwaito cewa shugaba Tinubu ya bayar da umarnin a biya ma’aikatan jami’o’i albashin su da aka riƙe musu na watanni amma har yanzu shiru babu labari.
