Connect with us

News

Kudin Kananan Hukumomi: Kotu Ta Bai Wa Gwamnatin Kano Wa’adin Kwana 7

Published

on

Gwamnan jahar Kano Abba Kabir Yusuf

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

 

Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta ba wa Gwamnatin Kano wa’adin kwanaki bakwai ta kawon dalilin da zai hana ta amsa bukatar shugabannin kananan hukumomin jihar 44 na hana gwamnatin amfani kudadensu.

Mai Shari’a Donatus Okorowo ne ya bayar da wannan umarni a makon jiya, bayan lauyoyin bangaorin sun gabatar da hujjojinsu a game da bukatar masu karar.

An Cafke Fasto Kan Damfarar Abokin Kasuwancinsa

Rikicin kudadaen kananan hukumomin ya kunno kai ne bayan majalisar zararwar jihar ta amince a biya kashi 70 na kudin aikin gina gadar sama a Kofar Dan-Agundi daga asusun kananan hukumomin jihar, a yayin daga gwamnayin jihar za ta biya ragowar kashi 30.

Aminiya ta ruwaito cewa Mai shari’a Okorowo ya ki amincewa da bukatar kananan hukumomin ta hana Gwamna Abba Kabir Yusuf amfani da kudaden nasu.

Advertisement

A zaman farkon na ranar 28 ga Disamba, 2023, alkalin ya umarci wadanda ake kara su bayyana a gabansa a ranar 3 ga watan Janairu su kawo dalilin da zai hana shi amsa bukatar masu kara.

Sannan ya amince da rokon da suka gabatar na mika takardar sammaci ga wadanda ake kara ta hannun wakilansu.

 

Dalilin Zuwa Kotu

 

Kungiyar Kananan Hukumomin Najeriya (ALGON) reshen kananan hukumomi 44 na Jihar Kano ne suka maka gwamnatin jihar a kotun ranar 27 ga watan Disamba, 2023.

Advertisement

Wadanda ake karar su ne gwamnatin jihar, babban lauyanta kuma kwamishinan shari’a da kuma Akanta-Janar na jihar.

Kananan hukumomin na neman kotu ta hana wadanda ake tuhuma taba kudadensu da ke asusun hadin gwiwa na jihar Kano, har sai kotu ta saurari karar da kuma yanke hukunci.

 

Zaman ranar Laraba

A zaman kotun na ranar Labara, lauyan masu kara, Ibrahim Nasarawa, ya shaida wa alkali cewa da farko an dage shari’ar ne domin wadanda ake kara su kawo hujjar da za ta hana kotu amsa rokon masu karar.

 

Advertisement

Nasarawa ya ce an ba wa wadanda ake kara takardar shari’ar bisa umarnin kotu, amma sun kasa gabatar da hujjojinsu a kwanaki ukun da kotun ta kayyade.

Don haka ya roki kotun da ta amince da bukatar masu kara kamar yadda doka ta 26, dokar kotu ta tanada.

 

Sai dai lauyan gwamnatin jihar, Hafeez Matanmi, ya kalubalance shi da cewa har yanzu bai ga jawaban da masu kara suka gabatar kan lamarin ba, don haka babu yadda zai iya bayar da kariya a kai.

 

Lauyan wanda ake kara na 3, Okechukwu Edeze, ya ce an yi masa bayanin lamarin ne kasa da sa’o’i 24 kafin zaman kotun na ranar, don haka ya nemi a dage sauraron karar.

Advertisement

Da yake yanke hukuncin, Mai shari’a Okorowo ya bayyana cewa, duk da cewa an mika wa wadanda ake kara sammaci yadda ya kamata a ranar 29 ga watan Disamba, 2023, amma ya amince da bayanin lauyansu cewa cewa wa’adin kwanaki uku da aka ba su su amsa ya shiga ranakun hutu

A saboda haka mai shari’a Okorowo ya baiwa wadanda ake tuhuma wa’adin kwanaki bakwai su kawo dalilasnu, sannan ya dage zaman shari’ar zuwa ranar 11 ga watan nan na Janairu.

 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending