News
Rundunar Ƴan sanda sun kama likitan da ya yi wa wata budurwa allurar zubar da ciki ta mutu a Kano
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Rundunar yansanda a jihar Kano ta ce ta kama wani likitan bogi mai suna Chidera Ugwu bisa zarginsa da yi wa wata mai juna biyu allura lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar ta.
Wata sanarwa da rundunar ta fitar, ta ce ta kama likitan bogin ne bayan samun wani rahoto kan wani matashi Ukasha Muhammad mai shekara 19 a ƙauyen Langel da ke ƙaramar hukumar Tofa, wanda ake zargi ya yi wa ƴar’uwarsa ciki, amma ya haɗa baki da Chidera domin yi wa matashiyar allura da nufin zub da cikin.
Ƴan ta’adda sun dasa bam a maƙabarta, sun halaka masu zaman makoki 103, sun jikkata wasu 141
Sai dai a cewar sanarwar, an samu akasi inda allurar da Chidera ya yi wa matashiyar ta yi sanadin mutuwarta.
A cewar rundunar, matasan biyu sun amsa laifin da ake zarginsu da aikatawa. Ko da yake, BBC a karan kanta ba ta iya tabbatar da hakan ba.
Sanarwar ta ce ana zargin Chidera Ugwu ya saba yi wa mata masu ciki allurar da take haddasa mutuwarsu, kamar yadda binciken da rundunar ƴan sandan ta ce ta yi ya nuna.
Daily Nigerian ta ruwaito cewa Rundunar ta kuma ce ta kama wani matashi Yusuf Haruna daga ƙaramar hukumar Dala wanda ake zargi da kashe wani fitaccen limami ta hanyar daɓa masa wuƙa.
Matashin ya daɓa wa limamin mai suna Mallam Sani Mohammed Shuaibu wuƙar ne a bayansa a lokacin da yake alwala.
A cewar sanarwar, an garzaya da limamin asibitin ƙwararru na Murtala Muhammad inda kuma likita ya tabbatar ya mutu saboda ciwon da ya ji.
Sanarwar ta bayyana cewa matashin ya yi aika-aikar ne saboda yadda limamin ya sha gargaɗinsa da ƴan tawagarsa kan su daina busa tabar wiwi a harabar masallaci.
Runudnar ta ce za ta gudanar da bincike kan laifukan biyu domin tabbatar da adalci ga waɗanda suka rasa rayukansu.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
