Connect with us

News

Sabuwar Doka: Da Ga Yanzu Duk Wani Ɗan NYSC Sai Ya Mallaki Lambar Rajistar Shaidar Ɗan Ƙasa NIN.

Published

on

DAGA MUSLIM YUNUS ABDULLAHI 

Hukumar yi wa kasa hidima, NYSC, ta fitar da sabuwar dokar cewa daga yanzu duk wanda zai yiwa ƙasa Hidima sai ya mallaki lambar rajistar shaidar ɗan ƙasa NIN.

Advertisement

Dokar ya biyo bayan wani rahoton sirri da Wani Umar_Audu ya fitar wanda ya fallasa kurakurai da dama da ake samu a fagen NYSC.

Dalilan da suka sa CBN ya ƙwace Bankin Union, Keystone da Polaris, ya naɗa masu sabbin daraktoci

Daraktan yada labarai da hulda da jama’a na NYSC, Eddy Megwa, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, ya bayyana cewa an ƙaddamar da sabuwar dokar ne biyo bayan wani taron da aka yi tsakanin hukumar ta NYSC, karkashin jagorancin Darakta Janar, Birgediya Janar Yushau Ahmed, da kuma Hukumar Kula da katin Shaidar Ɗan Kasa, NIMC, karkashin jagorancin Darakta Janar, Abisoye Coker-Odusote, wanda ya gudana a Abuja.

Advertisement

A wani labarin kuma Dalilan da suka sa CBN ya ƙwace Bankin Union, Keystone da Polaris, ya naɗa masu sabbin daraktoci

Babban Bankin Najeriya CBN ya sauya matsayarsa kan hada-hada da kuɗin intanet ko kuma cryptocurrency a ƙasar.

Advertisement

Jaridar Daily Trust ta ruwaito wata sanarwa da bankin ya fitar ranar Juma’a da ke umartar bankunan kasuwanci na Najeriya cewa su yi watsi da haramcin da ya saka kan amfani da kuɗin na crypto tu a 2021.

CBN ya ce yadda ake yayin kuɗin na crypto yanzu a faɗin duniya ya nuna irin buƙatar da ake da ita ta saka dokoki a kan sa.

Advertisement

“A watan Fabarairun 2021 CBN ya haramta wa bankuna da sauran cibiyoyin kuɗi amfani da cryptocurrency saboda almundahanar kuɗi da kuma ɗaukar nauyin ta’addanci,” in ji sanarwar.

“Sai dai kuma, abin da ke faruwa a duniya ya nuna cewa akwai buƙatar a kula da dukiyoyin hada-hada ta intanet wato Virtual Assets Service Providers (V/ASPs).”

Advertisement

Ya ƙara da cewa hukumar kula da hada-hada da hannayen jari za ta fitar dokoki da sharuɗɗan amfani da dukiyoyoin intanet ɗin.

Amma babban bankin ya jaddada haramcin yin kasuwanci, ko kuma mallakar asusun crypto ga bankunan kasuwancin su da kansu

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending