Connect with us

News

Ba mu da masaniya kan ficewar Jamhuriyar Nijar da Mali da Burkina Faso – Ecowas

Published

on

DAGA MARYAM BASHIR MUSA

Ƙungiyar Raya Tattalin Arzikin Ƙasashen Afirka ta Yamma, Ecowas ta ba ta samu sanarwa a hukumance ba game da ficewa mambobinta uku Nijar Mali da Burkina Faso ba.

Advertisement

Ƙasashen uku sun sanar da ficewarsu daga ƙungiyar ne cikin wata sanarwar haɗin gwiwa da aka karanta a gidan talabijin, inda suka zargi ƙungiyar da gazawa a taimaka musu wajen yaƙi da ta’addanci da kuma matsalar tsaro.

Yadda Mutuwar Wani Matashi Ya Girgiza Jama’a Sakamakon Wasiyyar Da Ya Bar Wa Iyayen Sa

To sai dai cikin wata sanarwar da Ƙungiyar ta fitar da maraicen ranar Lahadi, ta ce babu wata katarda da ƙasashen suka aike mata bisa wannna aniya tasu.  Ecowas ɗin ta ce tana aiki da waɗannan ƙasashen uku domin maido da su kan turbar dimokraɗiyya.

Advertisement

Sanarwar ta ƙara da cewa ƙasashen uku na da matuƙar muhimmanci ga ƙungiyar, don haka take ƙoƙarin ganin ta lalubo hanyoyin warware matsalolin da ƙasashen ke fuskanta.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending