News
Wani Malamin Furamare Ya Rataye Kansa A Jihar Kano
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Rahotanni daga jihar Kano na cewa wani mutum mai suna Nuruddeen ya rataye kansa a unguwar Gadon Kaya da ke karamar hukumar Gwale a cikin birnin Kano.
Tun da farko ana zargin Nuruddeen da ke aikin sana’ar koyarwa a makarantar Prestige Academy ya yanke hukuncin rataye kan sa ne bayan da ya samu labarin tsohuwar matarsa ta sake aure.
Ba mu da masaniya kan ficewar Jamhuriyar Nijar da Mali da Burkina Faso – Ecowas
Tun da farko an tsinci gawar mamacin ne sakale a ɗaya daga cikin ajujuwan makarantaar ta Prestige da ke layin Damisa a unguwar ta Gadon Kaya.
Kawo lokacin haɗa wannan rahoton Tuni jami’an rundunarr yan sandan Kano ta dauki gawar mamacin domin faɗaɗa bincike.
Ana samun ƙaruwar mutanen da ke kashe kansu a Kano, domin ko a cikin kwanakin bayan sai da aka samu irin wannan labari na wani mutum a unguwar Sauna kawaji da kuma garin Tsamiya de ke karamar hukumar Gezawa.
