News
Kotu Ta Aike Da Wani Tsoho Ɗan Shekaru 82 Gidan Yari A Kano
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Kotun majistray me lamba 90 dake zaman ta a madobi dake jihar karkashin Jagorancin maishari’a Haj. NADIYA ADO SALE ta ɗaure wasu mutane guda biyu inda ake tuhumar su da laifin hadin kai da ta’ammali da tabar wiwi wanda ya haɗa da Ilyasu Idris mai shakaru 82, da Yakubu Ɗalha 35.
Bayan da aka karanta masu kunshin tuhumar su ne, suka amsa. nan take ta karanto musu hukunci Inda ta daure malam ilyasu Idris mai shekaru 82, tsahon makwanni uku babu zaɓin tara, akan laifin hada kai wanda mai sharia ta duba tsufan sa da kuma rokon da ƴaƴansa da kuma shi kansa yayi a gabanta na neman afuwa da sassauci, sannan kuma akan tuhumar samun su da tabar wiwi kimanin ɗauri (Rob) 95 ta kuma daure shi wata shida ko zabin tara ta 50,000.
Majalisar Dokokin Jihar Kaduna Na Duba Yiwuwar Dawo Da Tsaftar Mahalli Na Karshen Wata
Maishari’a Nadiya ta kuma aike da abokin hulɗar tasa Yakubu Dalha gidan gyaran hali na tsahon shekara ɗaya babu zaɓin tara akan laifin hada kai da kuma wata 6 akan laifin samunsu da tabar wiwi ko zabin tarar dubu hamsin a gidan gyaran hali.
Maishari’ar ta hana zaɓin tarar ne kasancewar Wannan ba shine karo na farko da jami’an tsaro ke gurfanar dasu don girbar abunda suka shuka ba. Daka karshe tayi musu gargadi na zu zama mutanan kirki kuma su dauki Alkawarin daina saida kayan maye a wannan yanki na madobi jahar kano baki daya.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News6 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News3 days ago
Gwamna Abba Ya Ayyana Murtala Sule Garo A Matsayin Wanda Zai Yi Masa Takarar Mataimakin Gwamna A Zaɓen 2027
