News
Majalisar Dokokin Jihar Kaduna Na Duba Yiwuwar Dawo Da Tsaftar Mahalli Na Karshen Wata
DAGA MUSLIM YUNUS ABDULLAHI
Majalisar dokokin Jihar Kaduna ta fara nasari da shirye-shiryen dawo da dokar Tsaftar Mahalli na karshen wata-wata
Hakan ya biyo bayan taron bita da wayar da Kai da majalisar dokokin ta shirya da wasu hukumomi da kungiyoyi masu zaman kan su da masu ruwa da tsaki kan sauyin yanayi .
Hukumar EFCC ta bankaɗo ƙungiyar addini tana samo kuɗin ɗaukar nauyin ta’addanci
Hon. D Stingo, shine shugaban Kwamitin Tsaftar Mahalli da albarkatun kasa na majalisar dokokin Jihar Kaduna, ya ce Tsaftar Mahalli wani abu ne daya zama wajibi musamman a wannan lokacin da ake fama da kalubalen dumamar yanayi wanda ke jawo asara mai yawan gaske.
Yace sun shirya wannan zaman ne don tattaunawa da laluben hanyoyi ta yadda zaa shirya tsari mai kyau don ragewa da tunkarar kalubalen sauyin, musamman ganin cewa masana na hasashen wannan shekarar zata zama Mai zafin gaske, ganin cewar shekarar data gabata ta 2023 ita ce mafi dumama a tarihi.
Rahotanni na nuni da cewa da yake karin gaske kan taron na kwanaki biyu a lokacin da suke kammalawa, Honorable Mahmoud Lawal Bola Ege, Wanda shine Dan majalisa mai waklitar Birnin Zaria dake Jihar, yace zasu dawo da dokar da aka ajiye ta Tsaftar Mahalli Kuma zasu mayar da ita doka a fadin Jihar.
Taron yayi tsokaci kan yadda Al’umma zasu kaucewa abubuwan dake haifar da dumama da saresaren bishiyoyi ba bisa ka’ida ba da sauran hanyoyi.
