News
Gobara Da Ta Tashi A Kasuwar Yankatako Dake Kano Ta Kone Shaguna 21
DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta ce da sanyin safiya wata gobara ta kone kantuna 21 a kasuwar Yankatako da ke Rijiyar Lemo a karamar hukumar Dala a Kano.
Kakakin hukumar Saminu Abdullahi ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Kasa NAN cewa gobarar ta tashi ne da misalin karfe 02:00 na dare
Tsadar Rayuwa: Matsalolin mu ba daga Allah bane ba – Shehu Sani
A cewar Abdullahi, “Mun samu kiran waya da misalin karfe 02:00 na dare daga Hukumar Sadarwa ta Najeriya, NCC. cewa gobara ta tashi a kasuwar Yankatako.
Abdullahi ya ce shagunan 21 na kunshe ne a bangaren kayan daki na kasuwar.
Ya ce ba a samu asarar rai ba, kuma ana kan binciken musabbabin tashin gobarar.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News6 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News3 days ago
Gwamna Abba Ya Ayyana Murtala Sule Garo A Matsayin Wanda Zai Yi Masa Takarar Mataimakin Gwamna A Zaɓen 2027
