News
Kaduna Dai : ‘Yan Ta’adda Sun Yi Garkuwa Da Mata 15 Da Namiji Daya A Kudancin Kaduna
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
A ranar Asabar din da ta gabata ne wasu ‘yan ta’adda suka kai hari kan al’ummar Dogon-noma da ke karamar hukumar Kajuru a jihar Kaduna, inda suka yi garkuwa da mata 15 da namiji guda.
Daily Post ta ruwaito cewa wani mazaunin kauyen mai suna Istifanus, ya shaidawa manema labarai cewa da yawa daga cikin mazauna kauyen sun gudu zuwa yankunan da ke makwabtaka da su domin tsira da rayukansu a lokacin da ‘yan bindigar suka kai hari tare da harbe-harbe.
“Za mu iya tabbatar da adadi da yamma lokacin da za mu iya shiga ƙauyen. Maharan sun mamaye kauyen ne da misalin karfe 5:30 na safiyar ranar Asabar din nan da yawan gaske, inda suka rika harbi ba kakkautawa.
Wani tsohon shugaban karamar hukumar, Cafra Caino ya ce ba za a iya tantance adadin wadanda suka mutu ba.
“Har yanzu ba mu sami adadin wadanda suka mutu ba saboda mutanen yankin sun yi gudun hijira a lokacin da maharan suka mamaye al’umma. A cikin shekarar 2019, an kai wa al’umma hari inda aka kashe mutane 74, kuma a kwanan nan ne al’ummar kasar ke fuskantar hare-hare.
