Connect with us

News

El-Rufai: Nayi hasashen hakan zata faru  – Shehu Sani kan bashin $350m

Published

on

Tsohon Sanatan Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Tsohon Sanatan Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani, ya ce yayi hasashen haka zata faru akan bashin dala miliyan 350 da tsohon gwamna Nasir El-Rufai ya nema daga bankin duniya kamar wani Annabi .

Sani ya ce duk da gargadin da ya yi mutane sun ki saurara akan wannan lamunin.

Ƴan Sanda Sun Kama Mutumin Da Ya Daɓawa Ɗanuwansa Wuƙa Har Lahira.

Da yake jawabi ga manema labarai a ranar Lahadi, Sani ya ce jihar ba za ta shiga irin wannan hali ba idan gwamnatin El-Rufai ta yi kunnen uwar shegu.

Ya ce: “Lokacin hisabi ya zo ga kowane dan jihar,” Sani ya ce, yayin da yake mayar da martani kan kalubalen kasafin kudi a Kaduna.

“An zagi ni don na ce a’a ga wannan lamunin. Sa’ar hisabi tana nan ga kowane mutum a jihar Kaduna.

Advertisement

“Hakazalika, na gargadi al’ummar jihar nan, amma an ce musu kudin za su kawo ababan more rayuwa

“A yau, kuna iya ganin matsalolin da ke tattare da wannan lamuni.

“A yau jihar ta makale saboda wadannan kudaden da ba za mu iya biya ba.

“Mun karbo bashin dala miliyan 350 a lokacin da naira ta kasance N400 ga dala kuma za mu biya idan naira ta kai yau,” inji shi.

A makon da ya gabata ne Gwamna Uba Sani ya tayar da hankulan jama’a kan dimbin basussukan da ake bin jihar biliyoyin daloli.

A shekarar 2018, Sani da wasu Sanatoci biyu daga jihar Kaduna – Suleiman Hunkuyi, dan jam’iyyar APC mai wakiltar mazabar Kaduna ta Arewa; da Danjuma Laah na jam’iyyar PDP a shiyyar Kaduna ta tsakiya – sun ki amincewa da matakin da El-Rufai ya dauka na karbar bashin dala miliyan 350 daga bankin duniya.

Advertisement

Daga karshe Sani da Hunkuyi sun sha kaye a zaben da suka yi na sake tsayawa takara inda aka maye gurbinsu da Uba Sani da Suleiman Kwari wadanda suka nemi amince da wannan lamuni.

 

 

Daily Post

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending