Connect with us

News

Cutar Zazzabi Ta Yi Sanadiyyar Mutuwar Mutune 45 A Kauyen Jihar Kano

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Kimanin mutane 45 ne aka ruwaito sun rasa rayukansu sakamakon barkewar wata cuta mai ban mamaki a kauyen Gundutse da ke karamar hukumar Kura a jihar Kano.

Bayanai sun ce mata da kananan yara da tsofaffi ne cutar ta fi yi wa illa. Daga cikin alamun cutar akwai zazzabi mai zafi, amai da gudawa.

Idan Isra’ila ta kaiwa Iran hari babu ruwanmu a ciki – Amurka

Daily Trust ta ruwaito cewa Mazauna yankin sun bayyana damuwarsu game da karuwar mace-macen ba zato ba tsammani a cikin makonni biyun da suka gabata.

Sai dai lamarin ya zama mai firgitarwa yayin da al’ummar kasar suka fara binne mutane biyar a kullum, lamarin da ke nuni da cewa an samu matsalar rashin lafiya.

Abu Sani, wani mazaunin garin da ya rasa ‘ya’ya biyu, ya ce da farko ‘yan uwansa sun yi tunanin cutar zazzabin cizon sauro ce ke damun dansa dan shekara biyu, wanda ya mutu cikin bakin ciki duk da taimakon likitoci.

Advertisement

Jami’an lafiya a asibitin na Gundutse sun shaida wa wakilin jaridar Daily trust a ziyarar da suka kai cewa kawo yanzu an samu rahoton mutuwar mutane 20.

Daya daga cikin ma’aikatan lafiya a asibitin, wanda ya so a sakaya sunansa, ya ce tuni sun kai rahoton faruwar lamarin ga ma’aikatar lafiya ta jihar

Da aka tuntubi Jami’an yada labarai na Ma’aikatar lafiya na jihar Kano, Ibrahim Abdullahi, ya ce zazzabin materia ne ya kara da cewa ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano ainihin musabbabin mutuwar.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending