News
Babbar Magana: Magidanci ya kashe matarsa saboda wata zargi
SAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Rundunar ƴan sandan Ekiti ta fara binciken zargin kisa da wani magidanci ya ti wa matarsa saboda bata haihuwa.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Sunday Abutu, ya tabbatar a ranar Lahadi a Ado-Ekiti cewa kisan ya faru ne a ranar Asabar.
Tankar Mai Ta Kama Da Wuta A Birnin Fatakwal, Ta Halaka Mutane Da Dama
Premium Times ta ruwaito cewa Wani makwabcinsu ya shaida wa manema labarai cewa mutumin, wanda jami’in tsaro ne, da matarsa da ta mutu, wacce ke aiki a wani shagon sayar da magunguna, sun kulle kansu a cikin dakin kwanansu kafin aukuwar lamarin.
Ya ce ga dukkan alamu dai sun aiki babban ɗansu ne sanna suka bar karamin a wani ɗaki. Daga nan sai gardama da cacan baki ya ɓarke a tsakanin sai suka kaure da dambe sannan suka rika caka wa junansu wuka a jiki.
Makwabta sun yi kokarin shiga lamarin da raba su amma hakan ya gagara, domin sai da suka datse kofar shiga gidan sannan suka fara damben nasu.
Ta saman kwano wasu suka haura suka fasa sannan suka shiga ciki.
” Da aka samu aka shiga cikin gidan, an iske matar kwance malemale cikin jini, rai a hannun Allah, shima mijin duk jini jikinsa saboda sarar wuka da matarsa ta yi masa.
Makwabta sun yi kokarin gaggauta kai matar asibiti amma kuma daga bayabrai sai ya yi halinsa.
Yanzu dai ƴan sanda na gudanar da bincike akai.
-
News2 days ago
Shettima @60: Haƙurinsa, Biyayyarsa Sun Taimaka Wajen Ciyar Da Manufofin Shugaba Tinubu Gaba — Kwankwaso
-
News5 days ago
KANO:’Yan Mata Uku ’Yan Gida Ɗaya Sun Mutu A Kifewar kwale-kwale A Tiga
-
News5 days ago
Kwamitin Tsara Kundin Yakin Neman Zaɓen Gwamnan Kano Ya Yi Taron Tsare-tsare Manufofin Ci Gaban Jihar A Kaduna
