Connect with us

News

Ranar Yaki Da Cizon Sauro: Kusan Kashi 60 Cikin 100 Na Marasa Lafiya A Jihar Kano Cutar Maleriya Ce Ke Damun Su —Kwamishinan Lafiya

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Gwamnatin jihar Kano ta ce alkaluma sun nuna cewa cutar zazzabin cizon sauro kadai ta ja kusan kashi 60 cikin 100 na marasa lafiya a jihar Kano.

Advertisement

Haka zalika mutane 62 ne suka rasu sakamakon cutar zazzabin cizon sauro, yayin da mutane 474,565 suka kamu da cutar, daidai da kashi 98.8 cikin 100 kenan kuma aka yi musu magani da maganin da ake kira ACTs wanda shine aka tabbatar a matsayin sahihin maganin zazzabin cizon sauro.

Majalisar Dokokin Jihar Kano Ta Amince Da Dokar Gwajin Cutar Ƙanjamau Da Ta Sikila Kafin Aure

Kwamishinan lafiya na jihar, Abubakar Labaran ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai yayin bikin ranar maleriya ta duniya a asibitin koyarwa na Muhammadu Wase.

Advertisement

An yi kiyasin cewa a cikin shekarar 2023 kadai, sama da mutane miliyan 3.2 ne suka kai ziyara asibiti sakamakon barazanar zazzabin cizon sauro, wanda wata cuta ce da za a iya rigakafinta.

” Ta fuskar tattalin arziki, cutar zazzabin cizon sauro da mace-mace sun janyo asarar biliyoyin Naira na magunguna, rashin zuwa makaranta wajen aikin yi, zaman asibiti, da kuma kashe-kashen kudi.

Advertisement

“A 2023, yawan majinyatan da suka shafi cutar zazzabin cizon sauro ya kai 3,435,750, inda aka yi gwajin adadin masu cutar zazzabin cizon sauro a 3,247,651 da kuma 2,348,264 da aka tabbatar sun kamu da zazzabin cizon sauro (99.0%) da ACTs. A halin yanzu, an sami adadin mace-mace 448

Har yanzu ana iya cewa nazarin kimiyya bai kai ga cin nasara kan zazzabin cizon sauro, ko kuma cutar Malariya ba. A kasashen da ke da yanayi mai zafi, kwayar cutar da sauro ke bazawa na zaman wata babbar barazana ga rayuwar mutane, domin akalla mutane milliyan guda ke mutuwa daga cutar kowace shekara. Bisa wannan dalili ne Hukumar Kula da Lafiya ta Duniya ta kebe ranar 25 ga watan Afrilu a matsayin rana ta yaki da cutar.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending