Connect with us

News

Gwamnatin Tarayya Ta Kara Wa Ma’aikata Albashi

Published

on

Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI TUKUNTAWA 

Gwamnatin Tarayya ta amince da karin albashin ma’aikata daga kashi 25 zuwa 35 na ma’aikatan tarayya.

Advertisement

Tsarin albashin ya hada da ma’aikata (CONPSS), albashin cibiyoyin bincike (CONRAISS), albashin ‘yansanda (CONPOSS), albashin sojoji (CONPASS) da sauransu.

Ranar Yaki Da Cizon Sauro: Kusan Kashi 60 Cikin 100 Na Marasa Lafiya A Jihar Kano Cutar Maleriya Ce Ke Damun Su —Kwamishinan Lafiya

Idan dai ba a manta ba, tuni wadanda ke cikin manyan makarantun harkokin kiwon lafiya suka samu karin albashinsu da sauran ma’aikatan Jami’o’i.

Advertisement

Kwalejojin kimiyya da fasaha da na ilimi, karin albashinsu na karkashin tsarin CONOCASS.

Sashen kiwon lafiya, su sun samu tagomashin karin albashin a tsarin CONMESS.

Advertisement

Wata sanarwa mai dauke da sa hannun babban jami’in yada labarai na hukumar kula da albashin ma’aikata ta kasa (NSIWC), Emmanuel Njoku, a ranar Talata, ta ce karin albashin zai fara aiki ne daga ranar 1 ga watan Janairun, 2024.

Gwamnatin Tarayya ta kuma amince da karin kudin fansho daga kashi 20 zuwa 28 ga masu karbar fansho, wanda zai fara aiki daga ranar 1 ga watan Janairun, 2024.

Advertisement

Leadership ta ruwaito cewa Sanarwar na zuwa ne a jajibirin ranar ma’aikata ta 2024.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending