News
Mutane 15 Ne Suka Rasu Cikin Wanda Ake Zargin Wani Matashi Da Cinnawa Wuta Cikin Masallaci A Kano
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Ya zuwa yanzu mutane 15 cikin 30 da ake zargin wani matashi Nafi’u Abubakar da Konawa ta hanyar cinna musu wuta cikin Masallaci lokacin da suke sallar Asubah.
Lamarin da ya faru ne a dare Talata wayewar garin Laraba a Kauyen Tsamiya babba cikin karamar hukumar Gezawa a jihar Kano dake Arewacin Nigeriya.
Cin hanci da rashawa: Mu ’Yan Siyasa Idan Mun Sata Tare Da Mutane Mu Ke Rabawa – Ali Ndume
Shafi’u Abubakar yayi zargin zewa mutanen da ya cinnawa wutar mafi yawancinsu suna cikin Masallacin kuma sun cutar da shi a rabon gadonsu.
Idan za’a iya tunawa Jaridar Inda Ranka ta rawaito rundunar Yan Sandan jihar Kano ta bakin kakakinta SP Abdullahi Haruna Kiyawa na cewa sun fara gudanar da bincike kan lamarin.
Lamarin dai ya dauki hankalin mutane a jihar Kano wanda ya sa kowa yake bayyana ra’ayoyinsa dangane da lamarin.
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
