News
Tinubu ya faɗa wa matasa sai ya riga su zama shugaban ƙasa
Daga muhmmad muhmmad zahraddin
Tsohon gwamnan Legas kuma jagoran jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya faɗawa matasan ƙasar cewa za su yi shugabancin ƙasa amma sai bayan ya yi.
Fitaccen ɗan siyasar na Najeriya ya faɗi haka ne a ziyarar da ya kai wa Alaafin na Oyo Lamidi Adeyemi, a ranar Lahadi.
Tinubu ya buƙaci matasa su ba magabatansu dama.
“Kun toshe wa magabatanku dama tun kafin ku zama shugaban ƙasa, idan kun zama shugaban ƙasa fa, za ku kore mu ne a gari?”
“Sai kun tsufa za ku zama shugaban ƙasa, kuma sai na riga zama shugaban ƙasa,” in ji Tinubu.
Matasa a Najeriya sun daɗe suna fafutikar ganin sun kai ga madafan iko, da samun muƙaman siyasa.
-
Uncategorized7 days agoSamar Da Zaman Lafiya, Ayyukan Ci Gaba Sun Isa Shugaba Tinubu Ya Samu Wa’adi Na Biyu — Kwankwaso
-
News6 days ago
Aƙalla Mutane 40 Sun Mutu Bayan Kifewar kwale-kwale A Sokoto
-
News2 days ago
Pantami Da Yaransa Sun Fantama Min Ƙarya, Domin Babu Inda Na Ba Shi Haƙuri, Inji Hajiya Naja’atu Muhammad
