Connect with us

News

Majalisar dokokin Benue ta soke dokar biyan fansho na tsawon Rayuwa ga tsaffin Gwamnonin Jihar

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

A ranar Litinin ne Majalisar dokokin Jihar Benue ta soke dokar da ta baiwa tsaffin Gwamnonin Jihar da Mataimakan su damar karɓar fansho har na tsawon rayuwarsu.

Advertisement

Jaridar Inda Ranka ta samu rahoton cewa Majalisar ta 9 a watan Mayun 2023 ‘yan kwanaki kadan kafin ficewarsu ta zartar da kudurin dokar fansho mai cike da ce-ce-ku-ce na kara ma tsofaffin gwamnoni da mataimakansu wani kaso daga cikin lalitar Gwamnati.

Gwamnatin Tarraya Ta Dakatar Da Jirgin Nigerian Air Har Sai Baba-ta-gani

Sai dai majalisar ta 10 da ke Jagoranci a yanzu a zamanta na ranar Litinin ta soke dokar saboda a cewar majalissar ba a yi ta akan gaskiya ba.

Advertisement

‘Yan majalisar dai sun ce dokar ta sabawa ra’ayin mutane, kuma sun amince da soke dokar bayan tattaunawa da ‘yan Majalisar suka yi.

Don haka kakakin majalisar Aondona Dajoh ya amince da kudurin da Majalisar ta gabatar na soke dokar, tare da soke tanade-tanaden da tayi ma tsaffin zababbun gwamnonin jihar da mataimakansu da sauran batutuwan da suka shafi hakan.

Advertisement

Idan dai za a iya tunawa tsohon kakakin majalisar ta tara Engr Titus Uba ne ya jagoranci zaman Majalisar wadda tun farko ta amince da kudirin zuwa doka bayan da shugaban kwamitin harkokin kasuwanci da dokoki na majalisar na lokacin Hon Geoffrey Agbatse ya gabatar da shi a zauren Majalisar.

Kudirin ya tanadi sharuddan dokar da ya hada da biyan kudaden alawus-alawus na wata-wata a matsayin kudaden fansho na yau da kullun ga tsoffin gwamnoni da mataimakansu, wanda ya kasance kwatankwacin albashin gwamna mai ci a halin yanzu daga hadakar kudaden shigar Jihar.

Advertisement

Alawus na wata-watan zai zama daidai da Asalin albashin Gwamna mai ci a Jiha na har tsawon rayuwar su.

Haka zalika Mataimakin Gwamna zai ci gaba da karbar albashi duk wata daidai da ainihin albashin mataimakin Gwamnan mai ci har tsawon rayuwarsa wanda za a rika cirewa daga lalitar Gwamnatin Jihar.

Advertisement

Sai kuma Alawus alawus na Naira Miliyan 25 ga tsohon Gwamna da kuma Naira Miliyan 15 ga Mataimakinsa da za su rika amsa duk bayan shekara hudu 4.

Tsohon Mataimakin Gwamna kamar yadda dokar ta ce za a tanadar masa ma’aikata uku daya a matsayin mataimaki na musamman, ɗaya direba, ɗaya kuma mai tsaftace mashi gida, inda kuma za a samar masa da kudaden kula da lafiya a duk shekara, da chanja masu motocin da suke hawa masu daraja irin ta zamanin da ake ciki.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending