News
Kotu Ta Umurci Aminu Ado Bayero Da Ya Daina Ayyana Kansa A Matsayin Sarkin Kano

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Kotu a jihar Kano ta umurci Sarkin Kano na 15 Aminu Ado Bayero da ya daina ayyana kansa a matsayin Sarki ta kuma umurci jami’an tsaro da su fitar da shi daga gidan sarauta na Nasarawa.
SolaceBase ta ruwaito cewa kotun karkashin jagorancin mai shari’a Amina Adamu Aliyu ta ba da umarnin a ranar Litinin, 27 ga Mayu, 2024.
Majalisar dokokin Benue ta soke dokar biyan fansho na tsawon Rayuwa ga tsaffin Gwamnonin Jihar
Idan dai za a iya tunawa dai wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kano karkashin jagorancin mai shari’a A.M Liman ta bayar da umarnin dakatar da Muhammadu Sanusi II a matsayin Sarkin Kano a ranar Alhamis din da ta gabata ta kuma dokar kafa masarautu biyar da aka rusa a jihar.
Hakazalika, umarnin ya hana Alhaji Nasiru Ado Bayero, Dr. Ibrahim Abubakar II, Alhaji Kabiru Muhammad Inuwa da Alhaji Aliyu Ibrahim Gaya su gabatar da kansu a matsayin sarakunan Bichi, Gaya Rano da Karaye.
Wadanda ake tuhumar sun hada da Alhaji Nasiru Ado Bayero, Dr. Ibrahim Abubakar II, Alhaji Kabiru Muhammad Inuwa, Alhaji Aliyu Ibrahim Gaya, Sufeto Janar na ‘yan sanda, daraktan ma’aikatar tsaro ta kasa, jami’an tsaron farin kaya da Civil Defence da kuma rundunar sojojin Najeriya.
Yayin da masu karar suka hada da Babban Lauyan Jihar Kano, Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kano
-
News7 days ago
Wasu ’Yanbindiga Sun Yi Garkuwa Kimanin Yara 12 A Neja
-
News4 days ago
Majalisar Dattawa Ta Yi Watsi Da Shirin Farfaɗo Da Kamfanin Jirgin Saman Nigeria Air
-
News7 days ago
Jami’an NDLEA Sun Kama ‘Yan Nijeriya Biyu Mazauna Turai Da Suka Haɗiye Ƙunshin Hodar Iblis Guda 200 A Filin Jirgin Abuja
