Sports
Saudi League: Ronaldo Ya Karya Tarihin Cin Kwallaye A Kakar Wasa Daya
DAGA UMAR IBRAHIM HOTORO
Dan wasan gaba na kungiyar Al Nassr Cristiano Ronaldo ya karya tarihin cin kwallaye a gasar lig ta kasar Saudiyya a kakar wasa daya.
Ronaldo ya zura kwallo mai karfi a ragar Al Ittihad inda ya zura kwallaye 35 a raga.
Dan wasan mai shekaru 39 ya zira kwallaye biyu yayin da Al Nassr ta ci 2-0.
Wanda ya lashe kyautar Ballon d’Or sau biyar shima ya taimaka aka zura kwallaye 11 a wasanni 31.
Rikodin din da ya gabata shine kwallaye 34 da Abderrazak Hamdallah ya ci a kakar wasa ta shekarar 2018-19.
Yayin da Al Hilal ya lashe kambun SPL saura wasanni uku a kammala, Ronaldo da takwarorinsa za su yi wasan karshe a gasar zakarun Turai lokacin da za su kara da Al Hilal a wasan karshe na gasar cin kofin zakarun Turai.
Advertisements
