News
Daga Karshe Dai Gwamnatin Tarayya Ta Amince Da Biyan Tallafin Man Fetur
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
A Rahoton da ya bayyana an ji cewar gwamnatin tarayya ta bayyana yadda tallafin man fetur zai iya laƙume kimanin naira tiriliyan 5.4 a shekarar 2024
Daily Trust ta ruwaito cewa hakan ya banbanta da Naira Tiriliyan 3.6 d aka sare wa wannan ɓangare a shekarar 2023.
A jaddawalin shirin Accelerated Stabilization and Advancement Plan (ASAP) wanda ministan kudi, Wale Edun, ya gabatar wa shugaba Tinubu a ranar Talata, ya nuna cewa kiyasin kashe kudaden tallafin man fetur a shekarar 2024 ya kai Naira tiriliyan 5.4, kwatankwacin Naira tiriliyan 1. 8 tiriliyan Wanda hakan ya ninka fiye da adadin da aka kashe a 2023.
In ba a Manta ba Dai shugaba Tinubu ya bayyana karara tun ranar farko da ya hau mulki cewa gwamnatinsa ba za ta ci gaba da biyan tallafin man fetur ba.
