Connect with us

News

Rikicin Masarauta :  Aminu Ado Bayero ya umarci Hakimai su shirya hawan Sallah Babba

Published

on

DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA 

A ranar Talata ne sanarwar Alhaji Aminu Ado Bayero, daga masarautar Kano ta bayyana inda ya umarci Hakimai da Dagatai da su shigo cikin jihar don fara shirye-shiryen hawan sallah babba.

Advertisement

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da kwanan watan 10 ga watan June, 2024 da Galadiman Kano Alhaji Abba Sunusi ya rattabawa hannu.

Wani gini na makarantar kwalejin kimiyya da fasaha ta Kano ya kone kurmus

Sanarwar ta kuma bukaci Hakiman da su shigo cikin Kano da Dagatansu, mahaya da kuma dawakansu, domin shirye-shiryen fara hawan sallah babba.

Advertisement

Idan dai ba’a manta ba a makonnin da suka gabata, SolacBase ta rawaito cewa dambarwar masarautar Kano ta samo asali ne tun bayan da gwamnatin Kano ta tsige Alhaji Aminu Ado Bayero daga masarautar tare da maye gurbin shi da Muhammadu Sanusi II.Masarauta

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending