Politics
Ranar Dimokuraɗiyyar: Ƴan Nijeriya Fushi Suke Da Shugaba Tinubu
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Jam’iyyar PDP ta zargi jam’iyyar APC da janyo wa ‘yan Nijeriya wahala, inda ta yi iƙirarin cewa jam’iyyar APC ta gurgunta tsarin Dimokaraɗiyyar da MKO Abiola ya yi yaƙi don kafuwarta.
A wata sanarwa da sakataren yaɗa labarai na ƙasa Debo Ologunagba ya fitar, jam’iyyar PDP ta buƙaci ƴan Nijeriya da su yi zanga-zangar nuna adawa da tsarin Dimokuraɗiyyar jam’iyyar APC a yayin bikin ranar Dimokuraɗiyya ta bana.
Jam’iyyar PDP ta caccaki jam’iyyar APC da tauye kundin tsarin mulki, da magudin zabe, da danne ‘yan adawa, da kuma raunana cibiyoyin dimokuradiyya.
Wata Dalibar Jami’a Ta Jefo Jariri Da Ta Haifa Daga Bene Jim Kadan Bayan Haifarsa A Cikin Bandaki.
Ta yi Allah-wadai da ƙaddamar da katafaren gida na Naira biliyan ₦21b ga mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, adaidai lokacin da ake fama da durƙushewar ababen more rayuwa a ƙasar da kuma yawan rashin aikin yi.
Jam’iyyar PDP ta yi kira ga Shugaba Tinubu da ya yi tunani a kan halin da al’ummar ƙasar ke ciki, wanda ke nuna rashin jin daɗin jama’a kan yunwa da tsadar rayuwa, da kuma gyara manufofin da ke cutar da ‘yan kasa.
Sanarwar ta jaddada cewa ya kamata dimokuradiyya ta ba da fifikon ra’ayin jama’a, bin doka da oda, da kuma jin dadin ƴan ƙasa, inda ta zargi APC da yin watsi da waɗannan ka’idoji.
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
