News
Tirqashi: Abin Ya Wuce Satar Kaya A Cikin Unguwanni Har Ya Kaiga Ana Sata A Maƙabartu.
DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
Jami’an Bijilante sun kama wani mutum mai suna Bauhari da ake zargi da satar allunan Maƙabartar Unguwa Uku dake karamar Hukumar Tarauni dake Jihar Kano
Lamarin ya faru ne da misalin karfe 3:00 na dare yayin da Jami’an Bijilante suke gudanar da aikin su gefan makabartar dake kusa da INEC.
Gwamnatin Kano Ta Ba Da Umarnin Fitar Da Sarki Aminu Daga Fadar Nassarawa
Jaridar INDA RANKA ta ruwaito cewa wanda ake zargi “ya ce sana’ar sa itace gwan-gwan, Dan haka ya kan je makabarta dan gudanar da sace allunan alamomi na kaburbura.
Rahotanni na nuni da cewa Al,umma na zargin ƴan gwan-gwan ne ke zuwa su kwashe su allunan alamomi na kaburbura.
Sai dai wasu masu sana’ar ta tsince-tsincen kayan ƙarafan wato gwangwan a wannan yankin, sun musanta wannan zargi da ake yi musu.
Jihar Kano dai na da tarin maƙabartu da dama da babu hasken wutar lantarki, abin da wasu ke ganin cewa kan taimaka wajen bada mafaka ga masu zuwa su aikata miyagun laifuka akicinsu.
A wasu lokuta a baya, an sha samun waɗanda ke shiga maƙabartu a jihar da tsakar dare don tone gawarwaki, su ciri wasu sassan jikinsu dan wata mummunar manufa.
Adamu Abubakar Fiya Fiya Zonal Kwamandan Rundunar Bijilante dake Unguwa uku ya ce Rundunar ta samu nasarar cafke mutumin da ake zargin mai suna Bauhari .
Fiya Fiya ya ce bayan samun rahoton satar allunan maƙabarta a baya yasa suke tsaurara Tsaron maƙabartar bayan kammala Bincike zamu turasa wajan jami’an ƴan sanda.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
