Connect with us

News

Wata Babbar Motar Tirela  Ta Kashe Masu Sallar Juma’a 14, Tare Da Raunata Da Dama A Kano.

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC), reshen jihar Kano, ta tabbatar da mutuwar mutane 14 tare da wasu da dama da suka samu raunuka bayan wata babbar motar dako (Tirela) ta kwace tare da kutsa kai cikin jama’ar dake Sallar Juma’a a Kano.

Advertisement

SolaceBase ta rawaito cewa hatsarin ya faru ne a dai-dai lokacin da ake Sallar Juma’a a wani Masallaci da ke garin Imawa a karkashin karamar hukumar Kura.

Yayin Da Yan Najeriya Ke Fama Da Tsadar Rayuwa Za A Sayo Wa Shugaba Tinubu  Jirgin Da Bankin Jamus Ya Ƙwace Daga Hannun Wani Balarabe

FRSC ta bayyana cewa Direban motar ya gaza sarrafa ta, lamarin da ya kai ga ta kwace, ta kutsa kai cikin mutanen da ke Sallah kusa da bakin hanya.

Advertisement

A jawabin da kwamandan FRSC a jihar Kano, Ibrahim Abdullahi, ya fitar ta bakin kakakin hukumar, Abdullahi Labaran, ya bayyana cewa sun samu labarin afkuwar lamarin da misalin karfe 1:30 na rana.

Jawabin ya kara da cewa ya zuwa yammacin ranar Juma’a an binne mutum tara daga cikin wadanda suka rasa ransu yayin da wadanda suka samu raunuka suna samun kulawa a asibiti.

Advertisement

FRSC ta bayyana cewa ta gaggauta aika jami’anta zuwa wurin da abin ya faru domin su bayar da agajin gaggawa da kuma kulawa ta musammam ga wandanda abin ya shafa.

Hukumar FRSC ta mika sakon ta’aziyyar ta ga iyalan wadanda suka rasa ransu.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending