News
Ka Guji Maimaita Kuskuren Da Buhari Ya yi Na Son Zuciya – Shehu Sani Ya Gargadi Tinubu
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Tsohon Sanatan Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani, ya gargadi shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da ya guji maimaita kuskuren da tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi a fannin nada mukamai.
Shehu Sani ya ce ba kamar Buhari ba, ya kamata ya nada mukamai bisa cancanta.
Da yake gabatar da shirin a gidan talabijin na Channels Television na Politics Today, Tsohon dan majalisar ya zargi Buhari da son zuciya a lokacin da yake kan mulki.
Da yake jaddada cewa son zuciya ya kai kololuwa a Lokaci mulkin Shugaba Buhari , Sani ya yi mamakin dalilin da ya sa wasu Ministoci suka yi shekaru takwas a karkashin Buhari.
A cewar Sani: “Zan shawarci shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da ya yi taka-tsan-tsan kada ya tafka kura-kuran Shugaba Buhari Ya yi.
“A karkashin Shugaba Buhari, kana da ministoci da aka nada a kan mukamansu tsawon shekaru takwas; sun kasance tare da shi a zangon farko da na biyu, kuma babu wani sauyi a majalisar ministoci.
“Ko da an tsige shi, sai an dauki watanni uku zuwa hudu kafin a maye gurbin minista. Haka aka gudanar da mulkin kasar.
“A karkashin Buhari mun ga son zuciya a kololuwa inda aka nada mutane mukamai aka barsu a can ko da ba su yi komai ba.
“An ci gaba da rike shugabannin ma’aikata a ofis duk da gazawar da suka yi, kuma ta hanyar rike su, kun lalata sana’ar wadanda ke bayansu. Shekaru da yawa, an yi wa jami’ai da yawa ritaya don nada mutum ɗaya.”
-
Opinion4 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News6 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News3 days ago
Gwamna Abba Ya Ayyana Murtala Sule Garo A Matsayin Wanda Zai Yi Masa Takarar Mataimakin Gwamna A Zaɓen 2027
