News
Kotu Ta Daure Wani Manomi Da Ya Yi Wa Tsohuwa Mai Shekaru 65 Fyaɗe
DAGA YASIR KABIRU BASIRU
Kotun majistare dake Ado-Ekiti a jihar Ekiti ta daure wani manomi mai shekaru 45 Abajigbin Gbenga a gidan gyaran hali.
Alkalin kotun Dolamu Babalogbon wanda ya yi watsi da rokon sassauci da Gbenga ya nema ya yanke wannan hukunci ne bayan an same shi da laifin yi wa mata mai shekaru 65 fyade.
Ka Guji Maimaita Kuskuren Da Buhari Ya yi Na Son Zuciya – Shehu Sani Ya Gargadi Tinubu
Dan sandan da ya shigar da kara Sodiq Adeniyi ya ce Gbenga ya aikata wannan ta’asa a watan Afrilun 2024 a Ipole Iloro- Ekiti.
Adeniyi ya ce matan ta kira Gbenga domin ya yi mata feshi a gonanta.
“ A wannan rana da ya kamata Gbenga ya je ya yi aikin feshin sai ya roki matan ta kawo masa maganin feshin gida ya haɗa daga nan sai su garzaya ginar.
Ko da ta kawo masa maganin sai ya danneta ya yi lalata da ita.
Babalogbonya ce Gbenga zai zauna a gidan gyara hali har sai kotu ta kammala yin shawara da fannin dake gurfanar da masu aikata laifi irin haka na jihar.
Premium Times ta rawaito cewa za a ci gaba da shari’a ranar 31 ga Yuli.
-
News7 days ago
Na Shiga Siyasa Ne Domin Yi Wa Al’umma Hidima —Tsohon IGP Suleiman Abba
-
News5 days ago
An Tsare Kwamandan NSCDC Da Wasu Jami’an hukumar Da A Ke Zargi Da Sakaci A Mutuwar Masu Hakar Ma’adanai 37 A Neja
-
News4 days ago
Dakarun Soji Sun Ceto Ɗalibai 6 Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane A Katsina
