News
Gwamnatin Nijeriya ta kafa kwamitoci biyu da zasu yi yaki da ciwon zazzabin cizon sauro
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Gwamnatin tarayya ta kafa kwamitin bada shawara kan kawar da zazzabin cizon sauro a Nijeriya (AMEN) da kuma kwamitin ministoci na yaki da zazzabin cizon sauro a yunkurinta na kara kaimi wajen kawar da cutar zazzabin cizon sauro.
Ministan lafiya, Farfesa Ali Pate a shine ya bayyana Hakan a wajen taran kaddamar da kwamitin ba da shawara da kwamitin ministocin kasar nan
Pate , ya ce matakin ya zama wajibi bisa la’akari da gagarumar matsalar da cutar ke da shi a Nijeriya ta fuskar mace-mace,da Kuma yaduwar wasu cutukan tsakanin al’umma.
A cikin wata sanarwa ta hannun mai taimaka masa na musamman kan harkokin yada labarai da hulda da kasashen waje Tashikalmah Hallah, ministan ya jaddada cewa, duk da cewa ana iya yin rigakafi da kuma magance cutar,amma zazzabin cizon sauro na ci gaba da zama babban kalubale ga kasar.
Don haka, akwai bukatar cigaba da nemo hanyoyi tare da shawarwarin masana da zasu taimaka wajen kawo karshen sa.
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
