News
Rashan Cika Alkawari Yazama Dabi,ar Matasa Da Kuma Jagororin Al,umma
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Alkawari wani abune da yake da mutukutar muhimmanci ga rayuwar alumma baki daya, wanda yake zama cika makin tafiyar da alamuran rayuwa a yau da kullum.
Jaridar INDA RANKA ta ruwaito cewa duk da muhimmancin da alkwari yake da shi amma rashan cika alkawari yazama dabi,ar matasa da kuma jagororin al,umma.
A halin yanzu jama’a sun manta da muhimmancin cika alkawari, musamman a tarukan addini da siyasa da ilimi, wani lokacin harda tarukan da suka hada Gwamnoni da Malamai da Sarakuna, haka ake gudanar dasu ba’akan lokaci ba.
Haka zalika Allah subhanahu wata ala ya ambata inda yace “Ku cika alkawari! Dominshi alkawari abin tambayane a wajen Allah, kuma ku cika ma’auni! Idan za ku yi Awo to kuyi awo da ma’uni madaidaici, hakan alkhairi ne a gareku”.
Dan haka yana da kyau masu shirya taruka su rika zabar lokacin daya dace dasu, domin zama mutane na gari wajen cika alkawari tare da amfani da lokaci.
Domin a yanzu idan kaje wajen taron bikin Saukar karatun Alqur’ani ko makamanci sa da akasa karfe 10 to kafin a fara sai a shafe sama da awa biyu koma fiye da haka ana jira.
Yana da kyau al’ummar musulmi mu gyara mu kuma zama wadan da za’a rika koyi da mu bawai murika fada abakiba.
Ha ka kuma rashin cika alkawari yana zubar da kimar mutum da martabarsa a idon jama’a.
