Connect with us

News

Shugaban kasar amurka Joe biden ya kamu da cutar COVID 19

Published

on

DAGA KABIR BASIRU FULATAN 

 

 

Shugaban kasar Amurka Joe Biden ya kamu da COVID-19 a yayin da yake yaƙin neman zaɓe a Las Vegas kuma yana nuna alamu kaɗan na cutar, a cewar Fadar White House.

Sakatariyar Watsa Labarai ta White House Karine Jean-Pierre ta bayar da sanarwa ranar Laraba cewa ɗan takarar na jam’iyyar Democrat mai shekara 81 ya kamu da cutar ta korona

shugaban wata ƙungiyar kare hakkin fararen-hula ta Latino mai suna UnidosUS ya ce shugaban ba zai iya yin jawabi a wurin taron da suka gayyace shi sakamakon wannan cutar data kamashi sannan akwai bukatar killaceshi

Advertisement

Sanarwar tace yanzu An yi masa allurar riga-kafi kuma yanzu yana nuna alamun cutar ne in ji Jean-Pierre.

Trt Africa ta rawaito cewa za,a cigaba da killace shugaban ƙasar amma zai ci gaba da gudanar da ayyukansa kamar yadda suka kamata.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending