News
Dubun Dubatar Al’uma Ne Suka Fito Domin Raka Sarki Aminu Ado Rufe Taron Khatamar Al’qur’ani A Kano
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero yau ya halarci taron Khatamar karatun Al’qur’ani mai Tsarki dubu uku da aka gudanar a masallacin Juma’a na Sheikh Ishaq Rabiu dake Goron Dutse a birnin Kano.
Taron Khatamar Al’qur’anin mai tsarki wanda Khalifa Sheikh Nafi’u Ishaq Rabi’u ya shirya domin yiwa kasa da jihar Kano Addua’ar neman zaman lafiya da karuwar arziki da samun rangwame a halin da al’uma suke ciki yanzu na matsin rayuwa.
Jami’an DSS Sun Cafke Waɗanda Suka Yi Garkuwa Da Mahaifiyar Rarara A Dajin Maƙarfi
Manyan malamai da shehunnai sun gabatar da addu’oi na musamman a lokacin wannan taro na Khatamar karatun Al’qur’ani mai tsarki guda dubu uku.
Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya samu rakiya dubun nan magoya baya da masoya zuwa wajan taro.
