Connect with us

News

An Kama Yaro Dan Shekara 13 Bisa Laifin Bayar Da Bayanai Ga ‘Yan Bindiga A Katsina

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

Rundunar ‘yan sanda a jihar Katsina ta sanar da cewa ta kama wani yaro mai shekara 13 bisa zarginsa da aikata laifin bayar da bayanai ga ‘yan bindiga.

Advertisement

WIKKI TIMES ta ruwaito cewa an kama yaron ne biyo bayan sa ido da samun bayanan sirri a kan al’amuransa.

Mataimakin Gwamnan Jihar Edo, Philip Shaibu Da Aka Dawo Da Shi Kwanan Nan Ya Koma Jam’iyyar APC A Hukumance.

Kakakin rundunar ‘yan sanda a jihar Katsina, ASP Abubakar Sadiq Aliyu, shine ya sanar da hakan a wani jawabi da ya fitar ranar juma’a, 19 ga watan Yuli, 2024, a Katsina.

Advertisement

Jawabin ya bayyana cewa, “a ranar 3 ga watan Yuli, rundunar ‘yan sanda tare da hadon gwuiwar jami’an sa ido don tabbatar da tsaro a Katsina (KSCWC) sun samu nasarar kama wani Yaro mai shekara 13 da yake bayar da bayanai ga ‘yan bindiga a karamar hukumar Dandume.

“Yaron yana zaune ne a unguwar Sheikh Abdullahi a garin Dandume. An kama shi ne bisa laifin dake da alaka da taimakawa ‘yan ta’adda wajen gudanar da miyagun aiyuka.

Advertisement

“Yaron ya kware wajen bawa ‘yan bindiga muhimman bayanai a kan mutanen da suke yi wa mugun nufi. Ya shigo hannu ne bayan an tattara bayanan sirri a kansa tare da saka ido a kan motsinsa,” a cewar jawabin.

Jawabin ya cigaba da cewa; “Yaron ya amsa laifinsa da bakinsa yayin da ake tuhumarsa a ofishin ‘yan sanda tare da bayyana sunan wani Abba, wanda ya ce tare suke aiki, amma yanzu ya tsere bayan ya samu labarin an kama abokin laifinsa.”

Advertisement

A cewar Kakakin rundunar ‘yan sandan, wanda ake zargi ya kara bayyana cewa yana daga cikin gungun ‘yan bindiga da suka kai hari kauyen Unguwar Bawa, a lokuta da dama, tare da yin garkuwa da mutane da satar shanu.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending