News
Cacar Baki Ta Balle Tsakanin Jamiyyar APC Da Kuma Jamiyyar NNPP A Kano Kan Masu Zanga Zanga
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Shugaban jam’iyyar APC na jihar Kano Alhaji Abdullahi Abbas ya ce rashin iya mulki ne yasa gwaman kano a koda yaushe ya ke dora alhakin gazawarsa ga yan adawa .
Jaridar INDA RANKA ta rawaito Gwamnan jihar kano Alhaji Abba Kabir Yusuf a daren jiya ya zargi wasu yan jam’iyyar APCn kano da ingiza masu zanga-zangar da suke rika fasawa da sace kayan gwamnati da na al’umma a Kano.
Zanga Zanga: Ban nemi taimakon kowa ba kamar yadda wasu mutanan ke yadawa —Alaramma Malam Sa’idu
Abdullahi Abbas ya bayyana hakan ne cikin wani sakon murya da aka turowa manema labarai a yau Juma’a.
” Duk abun da ya faru sai ya ce mu ne, na fahimci kamar har yanzu ya kasa gane cewa shi yanzu mai mulki ne ba dan adawa ba, duk wata gazawarsa a matsayinsa na gwamna sai ya ce yan adawa ne”.
Shugaban jam’iyyar na APC ya ce ba wani dan jam’iyyar APC da yake da ruwa a abubunwan da suka faru a jihar, Inda ya ce gwamnan ne ya kirawo ruwa kuma ruwan ya kare akansa.
” Kowa yasan yadda malamai su kai ta fadawa al’umma illar yin zanga-zanga har ma suka ce haramun ce a Addinin Musulunci, Amma ranar laraba gwamnan kowa ya ji shi inda ya ke cewa a fito ayi zanga-zangar kuma shi zai fito ya karbe su, to shi ne suma matasan suka ga tunda an gayyace su bari su je su ci irin ganimar da yake ci “. Inji Abbas
Ya kara da cewa suna da labarin yadda wasu jami’an gwamnatin jihar kano suka yi taro da mafarauta kusan rukunonin 70, ” ka je ka bincika ko kasa yan sanda su bincika Maka, in kuma baka da labari to mu mun san Sanda aka yi da inda aka yi da kuma wadanda suka yi”.
Abdullahi Abbas ya kuma shawarci gwamnan da ya mai da hankali wajen yiwa al’ummar jihar Kano aiki kafin lokaci ya kure masa, maimakon daura alhakin gazawarsa akan yan adawa.
