Connect with us

Politics

Babu ƙofar juyin mulki, ku nemi wata hanyar sauya Gwamnatin Tinubu – Adams Oshiomhole yagayawa ƴan Najeriya

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

 

 

 

Sanatan Edo ta Arewa, Adams Oshiomhole, a ranar Laraba ya bayyana cewa babu wata dama da Sojoji za su kwace Mulki a Najeriya.

Oshiomhole ya ce ba zai yuwu wata ƙungiya mara tasiri ba ta nemi sauya tsarin Shugabanci ba a Najeriya.

Advertisement

Wasu masu zanga-zanga da ke fafutukar kawo ƙarshen Mulkin rashin adalci a Najeriya sun bukaci a kori Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu saboda halin kuncin da ƙasar ke ciki.

Sai dai da yake zantawa da manema labarai  jigon na Jam’iyyar APC ya ce “Babu yadda za a yi a canza Gwamnati ko kuma Sojoji suyi juyin Mulki, Ba zai yuwu wata kungiya mai ra’ayin rikau ta buƙaci a sauya tsarin Mulki ba.

“Na yaba da hakurin da Tinubu ya yi da yadda ya magance waɗancan batutuwa, inda Tinubu ya bayyanawa ƴan Najeriya cewa na saurare ku, kuma na ji matsalolin ku, amma zan so ganin mun aiwatar da tsare-tsaren mu domin hakan zai magance yunwar da ake fama da ita.

Babu wani lokaci da na yi kira da a sauya Gwamnati a cikin zanga-zangar da na yi, yanzu ina ganin ƴan Siyasa ne ke ƙoƙarin yin uwa makarɓiya da wannan lamari na zanga-zanga.

“Za a iya amfani da zanga-zangar lumana don neman canjin tsarin mulki amma ba canjin Gwamnati ba,” inji shi.

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending