Connect with us

News

KANO: Matasa Sun Fasa Rumbun Ajiya Inda Suka Kwashi Shinkafa Dake Da Hatimin Gwamnatin Tarayya

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

Wasu fusatattun matasa a unguwar Gandun Albasa da ke jihar Kano suka kai hari makarantar Islamiyya ta Wada Sagagi, inda suka yi awon gaba da shinkafa mai rubutun gwamnatin tarayya a jiki.

Advertisement

Hikima Radiyo ta ruwaito cewa wasu mazauna unguwar sun ce, matasan sun shiga gidan ne da talatainin daddare, domin kwasar shinkafar da ake zargin wadda gwamnatin tarayya ta aiko ne domin rabawa mabukata.

Dan Sanda Ya Kashe Amarya Dab Da Bikinta A Yayin Zanga-Zangar Adawa Da Tsadar Rayuwa A Kano

Makarantar dai, na zaune ne a tsohon gidan shugaban ma’aikata na fadar gwamnatin Kano, Alh Shehu Wada Sagagi.

Advertisement

Duk kokarin da Hikima Radio ta yi domin jin ta bakin shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin Kano Shehu Wada Sagagi da zargin ke alakantawa da kayan, lamarin yaci tura, amma shugaban makarantar Islamiyyar ta Wada Sagagi ya tabbatar da faruwar shigar matasan cikin makarantar tare da kwasar buhunhunan shinkafar.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending