News
Gwamnan Jihar Plateau Caleb Mutfwang, Ya Dakatar Da Wasu Kusoshi A Gwamnatinsa
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Gwamnan jihar Filato, Barr Caleb Mutfwang, ya amince da dakatar da wasu kwamishinoni biyu a majalisarsa nan take, sai dai babu wani dalili da ya bayyana akan dakatarwa.
Wata sanarwa da Daraktan yada labarai da hulda da jama’a Gyang Bere ya fitar, ya bayyana sunayen kwamishinonin suka hada da, Chysantus Dewam, kwamishinan ma’aikatar kasafin kudi da tsare-tsare ta tattalin arziki, da takwaransa na yawon bude ido Hon Jemima Tukur.
Gwamnan Jihar Plateau Caleb Mutfwang, Ya Dakatar Da Wasu Kusoshi A Gwamnatinsa
Sauran da ke cikin jadawalin dakatarwar sun hada da Hon Dio Lamul, mashawarci na musamman kan ayyukan raya karkara; kuma jami’in hulda da jama’a na mazabar Mikang, tsohon kakakin majalisar dokokin jihar Filato, Hon Moses Sule.
