News
Jerin Sunayen Jami’o’i 8 Na Kasar Benin Da Togo Gwamnatin Tarayya Da Ta Amince Da Nagartar Su
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa jami’o’i takwas ne kacal a kasar Benin da Togo da ta amince da nagartar su domin bayar da takardar shaidar kammala karatun digiri.
Farfesa Tahir Mamman, ministan ilimi, shine wanda ya sanar da hakan ranar Lahadi yayin da yake magana a wani shirin siyasa na gidan Talabijin din Channels.
A ranar Juma’a ne WikkiTimes Hausa ta rawaito cewa Farfesa Tahir, yayin wani taro na murnar cikar shekarar sa daya a matsayin minista, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya za ta soke takardun shaidar kammala karatu fiye da 22,500 da wasu jami’o’in kasashen biyu suka bawa ‘yan Nigeria
A cewar Ministan, an dauki wannan matakin ne yayin zaman majalisar zartarwa ta kasa wanda shugaban kasa, Bola Tinubu, ya jagoranta.
Tahir ya bayyana cewa matakin da gwamnati ta dauka yana daga cikin shawarwarin da kwamitin da aka kafa domin bankado badakalar takardun karatu ya bayar.
Ministan Ilimi: Tahir Mamman
A cikin watan Disamba na shekarar 2023 ne jaridar DAILY NIGERIAN ta bankado yadda ake cuwa-cuwar mallakar takardun shaidar kammala karatun jami’a daga kasar Benin da Togo.
Da yake magana a cikin shirin, Ministan ya ce gwamnatin tarayya ta amine da nagartar jami’o’i uku ne kacal a kasar Togo da kuma guda biyar a kasar Benin.
Ga jerin sunayen jami’o’in da Farfesa Tahir ya lissafa tare da bayyana cewa gwamnatin Nigeria ta amince da nagartar su da ingancin karatunsu;
Universite De Lome (kasar Togo)
Universite De Kara (Kasar Togo)
Catholic University of West Africa (Kasar Togo)
Universite D’abomey-Calavi ( Kasar Benin)
Universite De Parakou (Kasar Benin)
Universite Nationale Des Sciences, Technologis Ingenierie Et Mathematiques (kasar Benin)
Universite Nationale D’ Agriculture (Kasar Bernin)
Universite Africaine De Devlopment Cooperatif (kasar Benin)
Kazalika, Ministan ya jaddada cewa babu gudu babu ja da baya a kan shawarar da gwamnatin tarayya ta yanke a kan soke takardun shaidar kammala karatun digiri guda 22,700 da jami’o’in bogi a kasar Benin da Togo suka bawa ‘yan
Nigeria a tsakanin 2017 zuwa 2023.
