News
Matsalar tsaro: Kungiyar Amnesty International tayi Allah wadai da kama wani Matashi sabida wallafa wani faifan bidiyo

DAGA KABIR BASIRU FULATAN
Kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty International ta zargi gwamnatin jihar Sokoto da Hannu wajen kama wani Matashi mai amfani da shafukan sada zumunta mai Suna Shafi’u Umar Tureta.
Ta cikin wata sanarwa data fitar kungiyar ta zargi gwamnatin da amfani da karfin jami,an tsaro wajen kama matashin da yayi Suna sabida kawai ya wallafa wani faifan bidiyo na “bikin zagayowar ranar haihuwar matar gwamnan duk da matsalar tsaron da Jahar Sokkkoton ke fama da ita.
Kungiyar ta yi zargin ana shirin gurfanar da Shafi’u Tureta a gaban kotu, a kokarin neman zaman gidan yari na tsawon lokaci, domin a ba shi lokaci mai tsawo na kirkira tuhume-tuhumen da ake yi masa na bogi.
Dole gwamnatin jihar Sokoto ta gaggauta sakin Shafi’u Umar Tureta ba tare da wani sharadi ba.
Kungiyar ta ce Wannan abu da akayiwa Shafin,u take hakkin dan Adam ne Kuma ya Zama tillas gwamnatin jihar Sokoto ta gaggauta sakin Matashin domin Kungiyar bazata amince dacin zarafin Dan Adam ba.
Kungiyar ta Kuma bukaci gwamnatin data maida hankali wajen magance talauci, da yaran da ba sa zuwa makaranta da kuma tashe-tashen hankula a fadin Jahar Sakkwaton ke fama da ita da kawo karshen matsalar rashin tsaro a jihar.
Idan z,a tunadai jihar Sokkkoto na fama da Karancin matsalar tsaro inda koda a kwanan bayannnan saida Yan Bindinga suka kashe basaraken gargajiya,Kuma suka amshi Naira 60ml da Kuma mashinan hawa guda 5 kudin fansar Dan sarkin da sukayi garkuwa da sarkin tare.
Daily Trust
