News
YANZU-YANZU: Kwankwaso na shirin ficewa daga PDP zuwa NNPP
Daga yasir sani abdullahi
Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, na shirin sake ficewa daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar New Nigeria Peoples Party NNPP.
Tuni dai Sanata Kwankwaso a ranar Talata ya gana da shugabannin jam’iyyar NNPP a wani yunkuri na kammala zuwansa jam’iyyar da ake sa ran zai yi amfani da shi wajen neman takarar shugaban kasa.
Sakataren jam’iyyar na kasa mai barin gado, Ambasada Agbo Gilbert Major ne ya bayyana hakan a Abuja, a wajen taron kwamitin zartarwa na kasa (NEC).
Ya ce taron na da nufin daukar muhimman shawarwari da za su mayar da jam’iyyar gabanin babban zaben 2023.
A cewarsa, nan da ‘yan kwanaki gwamnan jihar Kano da ya yi sau biyu zai koma jam’iyyar tare da abokansa.
Ya kuma yi watsi da ba Kwankwaso tikitin takarar shugaban kasa kai tsaye, inda ya ce za a bai wa sauran masu son tsayawa takara.
#indaranka
-
News6 days ago
Matasa A Unguwar Gama Sun Yi Kira Ga Majalisar Dokokin Kano Ta Ladabtar Da Ɗan Majalisar Nassarawa Kan Zargin Cin Zarafin Gwamna
-
News6 days ago
Shugaba Tinubu Ya Ce Ba Zai Dawo Da Tallafin Man Fetur Ba Kuma Ba Ya Da-na-sanin Cire Shi
-
News5 days ago
DSS Ta Gurfanar Da Mutum Biyar Gaban Kotu Bisa Zarginsu Da Garkuwa Da ‘Yan NYSC 20 A Imo

