News
Gwamnatin Tarayya Ta Ci Amanar Mu Ta Ci Amanar ‘Yan Najeriya Kan Ƙarin Kuɗin Fetur – Kungiyar NLC
DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
Ƙungiyar Ƙwadago Najeriya (NLC), ta bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ta ci amanar su, kuma ta yaudare su kan ƙarin kuɗin fetur da aka yi a ranar Talata a gidajen man NNPCL.
Shugaban NLC Joe Ajaero ya bayyana haka a cikin wata sanarwar da ya fitar ranar Talata, inda a ciki ya ke cewa, “Lokacin da muka zauna da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya ba mu zaɓi biyu: “ko dai a maida mafi ƙanƙantar albashi Naira 250,000 amma mu maida litar fetur Naira 1,500 ko Naira 2,000. Ko kuma mu kai mafi ƙanƙantar albashi Naira 70,000, ba da tare da mun ƙara kuɗin litar fetur ba.”
Wani Harin Mayakan Boko Haram Kan Masallata Yayi Sanadiyyar Mutuwar Mutane 34 A Yobe
Gidajen man NNPC dai sun ƙara kuɗin lita daga Naira 600 zuwa Naira 897.
Har yanzu ba a bayyana dalilin yin hakan ba.
Ya ce NLC ta amince da mafi ƙanƙantar albashi a Naira 70,000 ba tare da an ƙara kuɗin fetur ba. Amma kuma abin mamaki ranar Talata sai aka yi ƙarin kuɗin fetur ɗin.
Matsalar Fetur Bayan An Sace Kuɗaɗen Gyaran Matatun Mai:
PREMIUM TIMES ta buga labarin cewa’ wani masani a harkokin mai ya ce an yi watandar biliyoyin kuɗin da aka riƙa warewa domin a gyara matatun man Najeriya
farfesan da ke zaune Amurka, Izielen Agbon, ya bayyana cewa duk an sace maƙudan biliyoyin kuɗaɗen da aka riƙe cirewa domin a gyara matatun ɗanyen mai huɗu na ƙasar nan.
Matatun dai su ne na Warri, Fatakwal, Legas da Kaduna.
Agbon ya yi zargin cewa waɗanda ake ɗora wa aikin kula da matatun man, su ne tantiran ɓarayin da ke sace kuɗaɗen.”
Agbon wanda ƙwararren injiniya ne, kuma Shugaban kamfanin Energy Equilibrium Inc., a birnin Dallas na Jihar Texas, ya bayyana haka a lokacin da yake tattaunawa a gidan talabijin na AIT, yayin da rashin jituwa ta taso ne tsakanin NNPC da Matatar Ɗangote. Masanin ya yi wannan bayani a ranar 23 ga Yuli.
Duk da cewa Najeriya na ɗaya daga cikin manyan ƙasashen da ke da arzikin ɗanyen mai, shekara kusan 30 har yau an kasa tace ɗanyen mai a ƙasar nan, amma kuma duk gwamnatin da ta hau mulki sai an riƙa ware maƙudan biliyoyin kuɗaɗen gyaran matatun mai.
Agbo ya ce rashin kula wajen gyara da kuma bayar da gyara ga ‘yan gidoga shi ne daga cikin dalilan da suka lalata matatun man Najeriya.
Bayan haka ranar Alhamis ce NNPC ta buga tandar neman ‘yan kasuwa masu zaman kan su waɗanda za a bai wa aikin kulawa da gyara da tafiyar da matatun man guda biyu.
NNPCL ya ce za a yi hakan ne domin a samu yawan man da ake buƙata a ƙasar nan.
A cikin sanarwar da NNPCL ya fitar a shafin sa na Tiwita, wato X, ya bayyana ƙa’idoji da sharuɗɗan da ke tattare da kamfanonin da ake so a damƙa wa matatun guda biyu.
Matatar Warri dai ta na da ƙarfin tace ganga 150,000 a kullum, ita kuma Matatar Kaduna na da ƙarfin tace ganga 110,000 a kullum. Su na cikin matatun ƙasar nan huɗu waɗanda suka kasance a mace shekara da shekaru ba su aikin komai.
Duk da an shafe shekaru masu yawa ana kashe masu maƙudan biliyoyin daloli da sunan gyara, an kasa gyarawa, wanda hakan ta sa tilas Najeriya ke shigo da fetur da gas daga waje domin amfanin cikin ƙasa.
Cikin Agusta 2021 dai gwamnatin Buhari ta bada kwangilar gyaran Matatun Mai na Kaduna da Warri kan kuɗi har Dala biliyan 1.5.
Cikin watan Agusta 2023 kuma Gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ta yi alƙawarin cewa Matatar Warri za ta fara tace ɗanyen mai daga ƙarshen watan Maris, 2024. Ita kuma ta Kaduna aka ce sai ƙarshen shekarar 2024.
