News
Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shattima Ya Gana Da Shuwagabannin NNPCL Kan Tsadar Mai Fetur
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima ya gayyaci karamin ministan albarkatun Man fetur, Sanata Heineken Lokpobiri, da Manajan Darakta na Kamfanin Man Fetur na Nijeriya (NNPCL), Mele Kyari, zuwa Aso Rock.
Taron wanda ya sami halartar mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Mallam Nuhu Ribadu da mataimaki na musamman ga Shugaban Bola Tinubu Kan harkokin yada labarai Abdul,az iz Abdul,aziz wanda hakan baya rasa nasaba da karin farashin Man Fetur.
Haka kuma a taron akwai wasu jami’an gwamnati daga ofishin mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima.
Karin farashin man fetur na baya-bayan nan ya sa farashin sufuri ya tashi sama da kashi 50 a manyan biranen Nijeriya.
Sabon karin farashin, wanda Kamfanin (NNPCL) ya aiwatar, ya tashi daga N855 zuwa N897 kowace lita, ya danganta da wurin da ake ciki, daga N568-N617 a baya.
‘Yan kasuwa masu zaman kansu sun maida farashin su zuwa tsakanin N930 zuwa N1,200 kowace litar man fetur
-
News5 days ago
KANO: Yara 24 Da Ake Tuhuma Da Laifi Sun Amfana Da Shirin Gyaran Tarbiya Maimakon Hukuncin Kotu A Watan Yuli
-
News4 days ago
ICPC Ta Wanke Femi Gbajabiamila Daga Zargin Badakalar Hukumar Bogi
-
News5 days ago
Jami’an Ƴansanda Sun Dakile Yunkurin Sace Jariri Da Wasu Ma’aikatan Asibiti A Jigawa
