Connect with us

News

Hukumar DSS ta saki Omoyele Sowore Shugaban Jaridar Sahara Reporters

Published

on

FB IMG 1726395948926

DAGA KABIR BASIRU FULATAN 

 

 

Hukumar jami,an tsaro ta DSS ta saki Omoyele Sowore mai rajin kare hakkin dan Adam mamallakin Jaridar Sahara Reporters kuma dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar African Action Congress (ACC) a zabukan 2019 da 2023.

Da safiyar yau Lahadi ne Sowore ya wallafa cewar jami’an DSS sun cafke shi a yayin da yake shigowa Najeriya amma daga bisani jami’an sun sallame shi kamar yadda ya bayyana a shafinsa na X.

Haka kuma hukumar kula da shige da fice ta kasa (NIS) ta dawomashi da lasisinsa na Kasa da Kasa fasfo da aka kamashi dashi a filin jirgin saman dake Legas.

Advertisement

 

Tun da safiyar yau Lahadin ne jami’an hukumar shige da fice ta Kasa suka tsare  Sowore a filin jirgin bisa zargin da hukumar takeye  akan da hannunsa a tada zaune tsaya a lokacin yin zanga -zangar matsin rayuwa.

Yanzu an sake ni. An dawo mini da fasfo na da komai,” in ji Sowore yayin da yake tabbatar da sakin sa.

Jirginsa dashi ya Iyalansa ya taso daga filin jirgin saman Washington Dulles da misalin karfe 6.14 EDT ya isa Legas da misalin karfe 9.43.

 

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending